Dan shekara uku ya kashe mahaifiyarsa bisa kuskure

Yana latsa kunamar bindigar nan take harsashi ya fito kuma ya shiga ta wuyan mahaifiyarsa.

Dan shekara uku ya kashe mahaifiyarsa bisa kuskure

Kofar shagon da abin ya faru

Wani yaro dan shekara uku ya kashe mahaifiyarsa bisa kuskure yayin da yake wasa da wata bindiga a wajen birnin Chicago da ke kasar Amurka.

Kamar yadda ‘yan sanda na gundumar Dolton suka bayyana, wannan abin takaicin ya faru ne ranar Asabar da karfe 8:30 na dare a wurin da ake ajiye motoci na wani katafaren shago.

Sanarwar ta ce, “yaron na zaune a kujerar baya ne, cikin motar mahaifinsa inda mahaifin nasa na zaune a kujerar direba tare da mahaifiyarsa a gaban motar.

“Ba a san yadda yaron ya iya fito da bindigar ba, amma rahotanni na cewa ya rika yin wasa da ita ne a kujerar bayan motar.

“Daga baya sai ya latsa kunamar bindigar kuma nan take harsashi ya fito kuma ya shiga ta wuyan mahaifiyarsa mai suna Deejah Bennett, inda ya kashe ta.”

BBC ya ruwaito cewa ’yan sandan Dolton sun ruga da matar zuwa Cibiyar Lafiya ta Jami’ar, sai dai da isarsu likitoci suka tabbatar da cewa ta riga ta cika.

Yanzu dai ana tuhumar mahaifin yaron kan mallakar bindigar bisa wannan tsautsayi da ya auku a Kudancin Dolton.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina