dan shekaru 17 ya hada keke mai inji

Mukhtar Muhammad Jawad wani matashi ne dan makaranta sakandare wanda ya hada keke mai inji wanda yake amfani da ita wajen zuwa makaranta a birnin Abuja.Aminiya ta gana da shi. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za mu so mu ji tarihinka?Da farko dai sunana Mukhtar Muhammad Jawad, an haife kimanin shekara 17 da suka […]

dan shekaru 17 ya hada keke mai inji

Mukhtar Muhammad Jawad wani matashi ne dan makaranta sakandare wanda ya hada keke mai inji wanda yake amfani da ita wajen zuwa makaranta a birnin Abuja.Aminiya ta gana da shi. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so mu ji tarihinka?
Da farko dai sunana Mukhtar Muhammad Jawad, an haife kimanin shekara 17 da suka gabata. Ina karatu a Makarantar Sakandare ta al’umma wato Kwaminiti a turance a unguwar Asokoro a tsakiyar birnin Abuja.
Aminiya: Shin ko ka taba koyon aikin kanikanci ne ko makamancin haka?
A’a, ban taba koyon ko wane irin aikin ba ko kadan. Ni dai na yi tunanin in kera ne kawai, sai kuma mahaifina ya ba ni kwarin gwuiwa, bai kushe ni ba. Amma ni mutum ne mai son kwancewa da gyara kayayyaki da na’urori ko injuna in sun lalace. Ta haka na fara. Na kuma yi tunanin ne domin ana dauka na ne daga gida a unguwan Maitama zuwa makaranta a Asokoro. Wannan ya sa na yi tunanin yadda zan rika zuwa makaranta ina dawowa da kai kaina. Shi ya sa na fara tunanin ya ya zan samarwa kaina abin hawa na kaina. Daga Maitama zuwa Asokoro zai kai kamar tifayar mintoci goma sha biyar a mota. Amma da na kera wannan sai nake zuwa makaranta da shi ina dawowa. Ka ga yanzu ba sai na jira an kawo ni ba, ko kuma an zo a dauke ni ba, wato na yi gaban kai na ke nan.
Aminiya: Nawa ka kashe wajen hada wannan keke mai inji din?
A’a, ba ni na kashe ba, mahaifina ne ya kashe kudin. Na sawo sabon injin yin markade ko kuma na masu yin faci kirar Honda GS 160 a kan Naira dubu 25. Na sayi giya-bos mai canja giya a kan naira dubu 15, tayan keke na baya a kan Naira dubu biyar da kan keke da kuma kudin walda sai dai na cire tayan keken gaba na keke na na sawa mashin din.
Aminiya: Ko ka yi amfani da Intanet don neman ilmi daga bidiyon da wasu suka saka?
Eh, na shiga don neman yadda zan mayar da wasu notoci da na kwance, amma na kasa mai da su, amma baya na kalli bidiyon, na mai da su sumul kalau.
Aminiya: Tsawon wane lokaci ka dauka don hada wannan keke mai inji?
Na kwashe kimanin wata guda, ina hadawa ina ballewa har aka cimma nasara. Hakan ya faru ne don ban shirya ba, wato na shiga kere-kere da rana tsaka ne, ba tare da shiri ba sam. Amma a yanzu na samu fahimta.
Aminiya: Kai ka yi waldan ko an yi maka?
Ina da aboki mai walda, sai na rinka kiran shi gida yana zuwa da kayan aiki yana yi mini waldan, mahaifina yana biyan shi. Shi ya sa ban san nawa aka kashe bangaren walda ba. Kuma yanzu na kwashe watanni uku ina hawan wannan mashin din daga gida zuwa makaranta. Amma ranar da na fara gwada mashin din, sai mahaifiyata ta yi ta murna, ta sa aka sawo Maltina ta raba wa mutane.
Aminiya: Ya kake tuka wannan keke mai inji din?
Idan na tayar, sai in murda sai ya fara tafiya.
Aminiya: Ko kana da wani buri?
Burina shi ne ina son in samu tallafi daga gwamnati, in zama mai dogaro da kaina ba mai aikin albashi ba, in dauki ma’aikata, in rinka hada wannan keke mai inji da yawa domin sayarwa jama’a a Najeriya da kasheshen Afirka don a saukakawa jama’a yin zirga-zirga.
Aminiya: Shin ko ka taba samun rauni ko wani hadari yayin hada wannan keke mai inji?
A’a, ban ji rauni ba tun da na fara har na kammala.
Aminiya: Shin ko wata hukumar gwamnati ko’yan kasuwa sun nemi hadin gwuiwa da kai?
A’a, ba wanda ya tuntubeni.
Aminiya: Shin ko mutane suna murna da wannan mashin naka?
Eh, shugaban makarantanmu Alhaji Said Ahmad da malamai duk sun yi murna. Sannan mutane da yawa suna tsayar da ni su tambaye in ba su amsa suna ta yin murna. Suna cewa, mashin ne ko keke?
Aminiya: Ya kake da sauran ababen hawa don ba shi da sigina na zaka bi hagu ko dama?
Iyayena sun ce in rinka sa hulan kwano, in rinka tafiya a hankali, in rinka bin gefen titi, kar in bi tsakiyan titi. Ina sahannu ne a matsayin alama in zan yi kwana.
Aminiya: Idan mutum yana son ka kera masa irin wannan mashin din, nawa zai baka?
Zan karbi Naira dubu 150.