Dan Shugaba Buhari ya yi hadari

Yusuf, babban dan Shugaba Buhari ya fadi a babur kirar power bike a garin Abuja. Kafar yada labarai ta DAILY NIGERIAN ce ta ruwaito labarin daga wani makusancin Yusuf, inda ta ce ya samu rauni sosai, wanda har ya suma a nan take. “Yusuf ya yi kokarin ya wuce abokinsa ne a kan babur din, […]

Dan Shugaba Buhari ya yi hadari

Yusuf, babban dan Shugaba Buhari ya fadi a babur kirar power bike a garin Abuja.

Kafar yada labarai ta DAILY NIGERIAN ce ta ruwaito labarin daga wani makusancin Yusuf, inda ta ce ya samu rauni sosai, wanda har ya suma a nan take.

“Yusuf ya yi kokarin ya wuce abokinsa ne a kan babur din, sai babur din ta kwace daga kan hanya. Nan take ya fadi ya suma na wani lokaci kafin aka sanar da uwargidan Shugaban Kasa Aisha,” kamar wata majiya ta sanar da DAILY NIGERIAN.

“Nan take ta bada umarni a kaishi asibitin Cedarcrest, inda yake ci gaba da jinya. Abin da muka tunanin shi ne raunin kai ba wai karaya ba. Ba mamaki a kaishi kasar waje nan bad a dadewa ba," inji majiyar, kamar yadda DAILY NIGERIAN ta ruwaito.