Dan ta’adda ya tsere a hannun ’yan sanda

Wani wanda ake zargi da hannu a kashe-kashen mutane a yankin Akinyele na Jihar Oyo ya tsere daga hannun ’yan sanda. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta ce mutumin wanda a baya ya amsa cewa yana da hannu a kashe mutum shida ciki har da wata mata mai juna biyu ya tsere ne a ranar […]

Dan ta’adda ya tsere a hannun ’yan sanda

Wani wanda ake zargi da hannu a kashe-kashen mutane a yankin Akinyele na Jihar Oyo ya tsere daga hannun ’yan sanda.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta ce mutumin wanda a baya ya amsa cewa yana da hannu a kashe mutum shida ciki har da wata mata mai juna biyu ya tsere ne a ranar 11 ga watan Agusta.

A baya mazauna yankin Akinyele sun yi zanga-zangar zargin sakin babban wanda ake zargin kafin daga baya Kakakin Rundunar Fadeyi Olugbenga ya karyata.

A watan Yuli ne rundunar ta fara gurfanar da mutumin bisa kashe-kashe da ake zargin hannunsa da wasu mutum biyu a ciki.

Sai dai sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Lahadi ta ce mutumin ya tsere daga wurin da ake tsare da shi don haka jama’a su yi hattara.
Ta kuma bukaci duk wanda ya gan shi ko yake da masaniya a kan inda yake da ya taimaka domin a sake cafko shi.