Murtala Garo: Dan takarar Ganduje na shirin ficewa daga APC
Ganduje ya je gidan Murtala Sule Garo da dare domin lallashinsa.
Sabuwar takadama ta kunno kai inda dan takarar kujerar mataimakin gwamnan Kano Murtala Sule Garo, wanda gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ke goyon baya na shirin ficewa daga jam’iyyar APC.
Aminiya ta gano cewa a cikin daren ranar Laraba Gwamna Ganduje ya isa gidan Murtala Garo domin lallashin shi ya janye yunkurinsa na ficewa daga jam’iyyar APC.
- ‘Matata da ’ya’yana suna haduwa su lakada min duka’
- NNPP ta tsayar da Abba Gida-gida takarar gwamnan Kano
Majiyarmu ta ce ko bayan ganawar, Murtala bai nuna hakikanin matsayinsa game da zama ko ficewarsa daga APC ba, bai bayar da wata gamsasshiyar amsa ba.
“Zai gana da makusantansa ya dauki matsaya, amma bai ji dadin abin da ke faruwa ba, amma bai fice daga jam’iyyar APC ba ko takararsa,” in ji majiyarmu.
Ganduje ya zabo Murtala, tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin ya zaman dan takarar kujerar mataimaki gwamnan jihar ga mataimakin gwamnan jihar mai ci, Nasir Gawuna, a zaben 2023 da ke tafe.
Idan ba a manta ba, Ganduje ya hakura da neman kujerar Sanata ne bayan Barau ya jingine aniyarsa ta neman takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano.
Majiyoyi sun ce Murtala Garo na ganin Barau a matsayin babban dan adawarsa kuma daya daga cikin shugabannin bangaren APC na G-7 da suka nemi karbe akalar jam’iyyar a jihar.
Saboda haka yake ganin bai kamata Ganduje ya karbi sanata Barau ba bayan hukuncin Kotun Koli da ya damka shugabancin jam’iyyar a hannun bangaren gwamnan.
Ana ganin Murtala ya damu da dadin yadda ake yawan ficewa daga jam’iyyar ta APC mai mulkin jihar ta Kano, lamarin da ke barazana ga takararsa ta 2023.
Wasu na ganin zai iya komawa jam’iyyar NNPP da ake rububin shiga a jihar, kamar yadda a baya-bayan nan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau ya koma.