Dan takarar da ya kai Obaseki kotu ya janye

Hon. Omoregie Ogbeide Ihama ya janye takararsa  ga Gwamna  Godwin Obaseki a zaben neman takarar kujerar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Edo. Omoregie Ogbeide ya janye wa Obaseki ne a ranar da ake zaben dan takarar jam’iyyar PDP gabanin zaben gwamna jihar na watan Satumba. Ya kuma ce zai janye karar da ya kai na […]

Dan takarar da ya kai Obaseki kotu ya janye

Hon. Omoregie Ogbeide Ihama ya janye takararsa  ga Gwamna  Godwin Obaseki a zaben neman takarar kujerar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Edo.

Omoregie Ogbeide ya janye wa Obaseki ne a ranar da ake zaben dan takarar jam’iyyar PDP gabanin zaben gwamna jihar na watan Satumba.

Ya kuma ce zai janye karar da ya kai na neman kotu ta hana gwamnan shiga zaben fitar da gwanin, bayan a baya ya lashi takobin ba zai janye daga zaben ba.

Kafin janyewarsa, Omoregie Ogbeide ya kai karar ne bisa hujjar cewa dadewar Gwamnan Obaseki a jam’iyyar PDP ba ta kai ta ba shi damar tsayawa takara ba.

Lamarin ya sa kotun dakatar da dakarar da Obaseki kafin washegari wata kotu ta ba shi izinin tare da umartar jam’iyyar da kuma hukumar zabe ta INEC da kada su kawo masa tarnaki.

Obaseki ya shiga sahun ‘yan takara a zaben a jam’iyyar PDP ne bayan uwar jam’iyyar ta yi masa rangwame jim kadan bayan shigowarsa jam’iyyar.

Gwamnan ya shiga jam’iyyar PDP ne bayan tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta hana masa shiga zaben fitar da gwani gabanin zaben gwamnan da ke tafe wa watan Satumba.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara