dan takarar Gwamna na Jam’iyyar SDP ya rasu

Saura kwanaki a gudanar da zaben bana dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa karkashin Jam’iyyar SDP, Rabaran Hakila Yarima ya rasu.  Rabaran Yarima ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar ne a ranar 6 ga Disamban bara, inda rahotanni suka ce ya rasu a 6 ga Janairun nan.Sakataren Jam’iyyar SDP na Jihar Adamawa Dokta John Luka […]

dan takarar Gwamna na Jam’iyyar SDP ya rasu
dan takarar Gwamna na Jam’iyyar SDP ya rasu

Saura kwanaki a gudanar da zaben bana dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa karkashin Jam’iyyar SDP, Rabaran Hakila Yarima ya rasu. 

Rabaran Yarima ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar ne a ranar 6 ga Disamban bara, inda rahotanni suka ce ya rasu a 6 ga Janairun nan.
Sakataren Jam’iyyar SDP na Jihar Adamawa Dokta John Luka ya shaida wa Aminiya cewa Rabaran Yarima ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ya kai shi ga kwanciya a asibiti.
Dokta Luka ya ce “Hakila ya rasu ne sakamakon ciwon hanta da ya yi fama da shi, kafin bikin Kirsimeti a Gombe kuma ya rasu ne a ranar 6 ga Janairun nan.”
Ya ce ya rubuta wasika cewa zai janye daga takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar sakamakon rashin lafiya da ke damunsa. Ya kuma kara da cewa jam’iyyar ta yi hakuri da shi ta zabi wanda ya fi cancanta domin maye gurbinsa a zaben na bana.
Sakataren ya ce sun rubuta wa Hukumar Zabe ta kasa (INEC) kan lamarin hade da wasikar da marigayin ya rubuta, kuma a yanzu haka jam’iyyar tana kokarin neman wanda zai maye gurbinsa.