Dan takarar Gwamna ya je kotun sauraron kararrakin zabe da shaidu 8,000

Yana rokon kotun da ta soke nasarar da APC ta samu a Jihar

Dan takarar Gwamna ya je kotun sauraron kararrakin zabe da shaidu 8,000

Adebutu

Mutumin da ya yi wa jam’iyyar PDP takara a zaben Gwamnan Jihar Ogun na 2023, Ladi Adebutu, a ranar Talata ya isa kotun sauraron kararrakin zaben Jihar da shaidu har guda 8,000.

Dan takarar dai na kalubalantar nasarar da Dapo Abiodun ya samu a zaben Gwamnan Jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.

A kwafin karar tasa mai lamba EPT/OG/GOV/03/2023, dan takarar ya ce ya shigar da karar ce saboda yana zargin ba a bi Dokar Zabe ta Najeriya ba a yayin zaben.

Alkalai uku ne dai suke sauraron karar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamidu Kunaza suka ci gaba da sauraron karar a ranar Talata.

Lauyan Ladi Adebutu, Goddy Uche (SAN) ne dai ya gabatar da shaidun wadanda ke cikin jakukunan ‘Ghana mas go’, a gaban kotun wacce ke zama a Kotun Majistare da ke Isabo a Abeokuta, babban birnin Jihar.

Ya roki kotun da ta karbi hujjojin sannan ta yi amfani da su. Lauyan ya ce gabatar da shaidun ya biyo bayan bukatar hakan da kotun ta yi daga bangarorin shari’ar guda biyu.

Goddy ya kuma ce ya mika wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Gwamna Abiodun da jam’iyyar APC wani kundi mai shafi 98, wanda eke dauke da cikakkun dukkan hujjoji da shaidun da za su gabatar a gaban kotun.

Shaidun a cewarsa sun hada da wasu fom-fom na INEC da rahoton na’urar BVAS da fama-faman ECA da rajistar masu zabe da kuma sakamakon da aka dora a shafin INEC na intanet.

Sai dai lauyan Gwamna Abiodun, Kehinde Ogunwunmiju, ya yi kira ga kotun da ta yi fatali da shaidun saboda ba su bi ka’idojin da ya kamata ba.

Daga nan ne Mai Shari’a Hamidu Kunaza ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa nan da ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.