Dan takarar Gwamnan APC a Kogi ya dauki malamin Firamare a matsayin Mataimaki

Wanda aka zaba din kuma shi ne Shugaban NUT a Jihar

Dan takarar Gwamnan APC a Kogi ya dauki malamin Firamare a matsayin Mataimaki

Yahaya Bello da Usman Ododo

Dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a karkashin jam’iyyar APC, Usman Ododo, ya zabi malamin Firamare, Salifu Joel a matsayin Mataimakinsa a zaben 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Salifu dai yanzu haka shi ne mai rike da mukamin Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), kuma Ma’ajin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen Jihar.

Da yake jawabi yayin bikin da aka yi a fadar gwamnatin jihar da ke Lokoja, babban birnin Jihar, Gwamnan Jihar, Alhaji Yahaya Bello, ya ce an zabe shi ne a koakarin jam’iyyar APC na tafiya da kowa don ciyar da Jihar gaba.

Gwamnan ya kuma ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen tabbatar da jam’iyyarsu ta kai ga gaci a zaben Gwamnan Jihar da ke tafe.

Yahaya Bello ya kuma ce, “APC za ta bi duk hanyar da ta dace wajen tabbatar da jam’iyyarmu ta lashe zaben Gwamnan da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba, musammman saboda gwamnatina ta yi rawar gani a fannin ayyukan raya kasa, bunkasa ilimi da kiwon lafiya da dai sauransu.

“Mun yi wa mutanen Kogi abin kirki, a don haka ne muke bukatar kuri’unsu a zaben mai zuwa.

Gwamnan ya kuma ce siyasar kabilanci ko ta addini ba ta da muhalli a Jihar, inda ya shawarci ’yan siyasar Jihar da su guji yin duk wani kalami da zai iya saka su a tsaka mai wuya wata rana. (NAN)