dan takarar Gwamnan Filato na PDP a zaben 2015 ya rasu

dan takarar Gwmanan Jihar Filato na Jama’iyyar PDP a zaben 2015, Gyang Pwajok, ya rasu. Babban Jami’in yada labaran kungiyar yakin neman zabensa, Chuwang Dung ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari. Sai dai ya ce iyalan marigayin Mista Pwajok za su tabbatar ds alamarin. Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES, cewa, Mista Pwajok ya […]

dan takarar Gwamnan Filato na PDP a zaben 2015 ya rasu
dan takarar Gwamnan Filato na PDP a zaben 2015 ya rasu

dan takarar Gwmanan Jihar Filato na Jama’iyyar PDP a zaben 2015, Gyang Pwajok, ya rasu. Babban Jami’in yada labaran kungiyar yakin neman zabensa, Chuwang Dung ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari. Sai dai ya ce iyalan marigayin Mista Pwajok za su tabbatar ds alamarin.

Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES, cewa, Mista Pwajok ya rasu ne a wani asibitin kasar Indiya.
Mista Pwajok dai tsohon dan majalisar dattijai ne, kuma ya yi takarar neman kujerar gwamna a karkashin tutar jam’iyyar PDP a babban zaben 2015.
Ya fadi zaben ne bayan da suka fafata da Simon Lalong na jam’iyyar APC, wanda kuma a halin yanzu shi ne gwamnan jihar.
Mista Pwajok ya gaji marigayi danmajalisar dattijai Gyang Dantong, wanda ya rasu bayan ya fita daga wajen binne gawar wadanda ’yan harin kunar bakin wake suka kashe a BarikinLadi cikin shekarar 2012.