dan takarar Gwamnan SDP ya ce ana shirin kashe shi

dan takarar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar SDP Mista Dabid Sabo Kente ya ce wasu ’yan siyasa da ke adawa da tsayawarsa takarar Gwamna na nema kashe shi. dan takarar ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishin kamfen dinsa da ke Jalingo.Ya ce wadanda ke adawa […]

dan takarar Gwamnan SDP ya ce ana shirin kashe shi
dan takarar Gwamnan SDP ya ce ana shirin kashe shi

dan takarar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar SDP Mista Dabid Sabo Kente ya ce wasu ’yan siyasa da ke adawa da tsayawarsa takarar Gwamna na nema kashe shi.

dan takarar ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishin kamfen dinsa da ke Jalingo.
Ya ce wadanda ke adawa da tsayawarsa takarar Gwamna nan sun yi yunkurin halaka shi a lokuta daban-daban kuma har yanzu suna niyyar su halaka shi, amma a cewarsa ba za su yi nasara ba.
Mista Dabid Sabo Kente ya ce a ’yan kwanakin baya ma har janye kusan dukan jami’an tsaronsa aka yi kuma ya san haka din an yi ne domin samun saukin halaka shi.
Ya kara da cewa ganin haka ne sai ya garzaya zuwa wurin Babban Sufeton ’Yan sandan kasa inda ya shaida masa cewa an janye kusan jami’an tsaron da ke aiki a karkashinsa.
Ya ce Babban Sufeton ya ba shi wasu ’yan sandan kwantar da tarzoma sannan ya rubuta wa Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Taraba wasika kan lamarin.
dan takarar ya ce a halin da ake ciki masu adawa da shi suna yada jita-jitar cewa ya janye daga takarar da yake yi ya bar wa dan takarar Jam’iyyar PDP, Mista Darius Ishaku.
Mista Kente ya ce yana nan daram yana takara kuma bai taba farta cewa ya canja ra’ayinsa kuma ba zai taba barin takarar da yake yi ba, balle ya sauka ya bai wa wani dan takara damarsa ba.
“Duk wanda ya ce na janye daga takarar da nake yi mahaukaci ne kuma ba ni da ninyar yin haka ina nan daram ina yin takarar Gwamnan Jihar Taraba,” inji Kente.
dan takarar ya nuna takaicin yadda aka cusa addini a cikin siyasar jihar inda ya zargi kungiyar Kiristocin ta kasa (CAN) reshen jihar da hassada wannan matsala.
A cewarsa matsalar ta soma ne a lokacin da ita kungiyar ta yi ikirarin cewa tana goyon bayan dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP Mista Darius Ishaku shi kadai.
Ya ce wannan mataki yana da hadarin gaske domin jihar ta Taraba na da mabiya addinan Musulunci da Kiristoci da masu addinin gargajiya. Ya ce yin haka zai raba kawunan al’ummar jihar domin duk wanda zai jagoranci jihar dole ne ya kasance yana la’akari da cewa akwai hakkin daukacin jama’ar jihar a wuyansa.
“Burina shi ne in kasance shugaban kowa da kowa ba na bangare daya ba, zan kasance mai adalci ga daukacin al’ummar jiha ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba,” inji shi.
Ya ce a tarihin jihar ba a taba samun lokacin da kawunan mabiya addinin Kirista ya rabu irin wannan lokaci ba, inda ya ce da yawa daga cikin mabiya addinin Kirista a jihar sun nesanta kansu daga ikirarin kungiyar Kiristocin wanda a fili ya nuna irin rarrabuwar kawunan da ke tsakanin Kiristocin jihar.
Ya ce akwai bukatar ganin cewa kungiyoyin addinai sun maida hankalinsu wajen hada kan al’umma ba raba kawunansu ba.