Dan takarar kai-da-halinka zai kawo karshen kama-karyar jam’iyyu-Sanata Oduah

’Yar Majalisar Dattijai ta Tarayya, Sanata Stella Oduah, ta ce amincewa da majalisar ta yi da dan takarar kai-da-halinka a gyaran fuskar da suke yi wa kudin tsarin mulkin Najeriya zai taimaka wajen rage kama-karyar da jam’iyyu suke yi wajen zaben dan takarar a lokacin zabe. Sanata Oduah wacce take wakiltar mazabar Anambara ta Arewa […]

Dan takarar kai-da-halinka zai kawo karshen kama-karyar jam’iyyu-Sanata Oduah

’Yar Majalisar Dattijai ta Tarayya, Sanata Stella Oduah, ta ce amincewa da majalisar ta yi da dan takarar kai-da-halinka a gyaran fuskar da suke yi wa kudin tsarin mulkin Najeriya zai taimaka wajen rage kama-karyar da jam’iyyu suke yi wajen zaben dan takarar a lokacin zabe.
Sanata Oduah wacce take wakiltar mazabar Anambara ta Arewa ita ta bayyana haka yayin da take ganawa da kamfanin dillacin labarai na Najeriya a Abuja.
Ta ce sanya lamarin a cikin kundin tsarin mulki zai baiwa ’yan Najeriyar zabar mutumin da suke son ya wakilce su.
Ta bayyana yakinin cewa kudurin dokar zai kai gaci kuma zai zama wata kafa da za ta baiwa ’yan takara da masu zabe ’yanci.
“A karon farko mutane za su zabi wadanda suke so ba jam’iyya ba. Hakan zai zama wata yarjejeniya tsakanin ’yan takara da masu zabe. Saboda haka, idan aka zo gaba-da-gaba, masu zabe za su tambayi alfanun da dan takara zai yi musu idan suka zabe shi”. Inji ta