Dan takarar kujerar shugaban kungiyar Miyetti Allah ya nemi tubarrakin Sarkin Sasa

daya daga cikin ’yan takara shida na kujerar shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah na kasa baki daya, Alhaji Muhammed Kiruwa, Ardon Zuru ya fara yakin neman goyon baya da jihohi shida na Kudu maso Yamma, a yayin da ya ziyarci fadar Sarkin Sasa, Sardaunan Yamma, Alhaji Haruna Maiyasin domin neman tubarraki. Tawagar ta hada […]

Dan takarar kujerar shugaban kungiyar Miyetti Allah ya nemi tubarrakin Sarkin Sasa
Dan takarar kujerar shugaban kungiyar Miyetti Allah ya nemi tubarrakin Sarkin Sasa

daya daga cikin ’yan takara shida na kujerar shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah na kasa baki daya, Alhaji Muhammed Kiruwa, Ardon Zuru ya fara yakin neman goyon baya da jihohi shida na Kudu maso Yamma, a yayin da ya ziyarci fadar Sarkin Sasa, Sardaunan Yamma, Alhaji Haruna Maiyasin domin neman tubarraki.
Tawagar ta hada da dan takarar mukamin sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Baba Usman Ngalzarma da mai neman kujerar mataimakin shugaba na farko, Alhaji Husaini Bosso da Sarkin Shanun Gombe, wanda shi kadai yake neman kujerar ma’aji.
Tawagar ta gana da sarakunan Fulani da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na jihohin Yamma, inda ta bayyana dalilan yakin neman zaben.
A fadar Sarkin Sasa, Alhaji Kiruwa ya bayyana alhininsa kan, “Irin rikon sakainar kashi da ake yi wa al’ummar Fulani makiyaya, lamarin da shi ne babban dalilin da za mu yi fafutukar magancewa, idan Allah Ya ba mu nasarar jagoranci. Wannan kuwa yana bukatar goyon bayanka, amma idan ka dakatar da mu, ina tabbatar maka, za mu amshi umarninka da hannu biyu. Muna neman shawararka, a matsayin uba, wacce za ta kai mu ga kara tsoron Allah da yin adalci da kwatanta gaskiya, har mu kai ga nasarar ceto hakkin miliyoyin al’umar Fulani, wadanda Allah Ya azurta da albarkatun da Najeriya take alfahari da su, wadanda aka mayar gugar yasa.”
Ya ce a lokacinsu za su kara kaimi wajen ganin an samar da burtaloli don makiyaya; a inganta ilimin yaransu; a samar da tabbataccen tsaro daga salwantar rayuka da dukiyoyinsu; saboda lokacin ne kungiyar ta Miyetti Allah, za ta kara karfi sosai.
A jawabinsa, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudu, ya yaba wa tawagar kan wannan ziyara. Ya kuma jinjina musu da fitowarsu ta yakin neman zabe kan kyawawan manufofinsu, “Ina rokon Allah Ya ba ku sa’ar wannan fafutuka. Ina ba ku tabbacin hadin kai da goyon baya, musamman wajen kare hakkin ’yan uwa da ke zaune a wannan sashe.”
Sarkin ya tunatar da shugabancin jama’a yana bukatar gogewa da yin adalci tare da hakuri. “Jagorancin al’ummar Fulani yana da wuyar gaske, musamman saboda rashin hadin kawunansu; da rashin son yin amfani da dukiyarsu wajen cimma buri,  dole sai kun tashi tsaye wajen wayar da kan jama’ar da kuke so ku yi musu jagoranci su fahimci manufofinku da na hukuma.”