Dan takarar Mataimakin Gwamnan Katsina a NNPP ya yi murabus

Har yanzu ina nan a matsayin dan jam’iyyar domin kuwa ba fita na yi ba.

Dan takarar Mataimakin Gwamnan Katsina a NNPP ya yi murabus

Dan takarar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina a jam’iyyar NNPP, Dokta Muttaka Rabe Darma ya yi murabus.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga hedkwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) reshen Jihar Katsina.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Aliyu ya ce dan takarar ya kawo masu takarda a rubuce yana mai bayyana cewa ya ajiye takararsa a jam’iyyar.

Aminiya ta nemi ta tuntubi Dokta Muttaka don jin ko me ya yi zafi har ya sa ya dauki wannan mataki, inda ya bayar da amsar cewa a tuntubi jam’iyya.

Sai dai ya ce har yanzu yana nan a matsayin dan jam’iyyar domin kuwa ba fita ya yi ba.

Kazalika, ya ce takarar dai ce ya ajiye domin tasa ba ta zo daya ba da dan takarar Gwamnan, Injiniya Nura Khalil.

Ya yi zargin cewa ya lura dan takarar gwamnan ba mutumin da za a tafi tare da shi ba ne saboda rashin kirkin shi.

Wannan mataki da Dokta Muttaka ya dauka, masharhanta na ganin cewa ya karya jam’iyyar ta NNPP a inda ba gaba, domin ya yi haka a kurarren lokaci.

Duk wani kokari na ji daga ita jam’iyyar ya ci tura domin babu wanda ya yi magana a kan wannan lamari.

Wakilin ya kalato cewa jam’iyyar ta shirya taron ganawa da manema labarai don sanar da halin da ake ciki, amma daga bisani hakan bai wakana ba kuma babu wani bahasi da ya biyo baya.