Dan takarar NNPP ya maka jam’iyyar da INEC a kotu

Dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Gombe a Jam’iyyar NNPP, Auwal Isiyaku Seiko, ya maka jam’iyyar a gaban babbar kotun jihar.

Dan takarar NNPP ya maka jam’iyyar da INEC a kotu

Dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Gombe a Jam’iyyar NNPP, Auwal Isiyaku Seiko, ya maka jam’iyyar a gaban babbar kotun jihar.

Auwal Seiko, ya shigar da jam’iyyarsa da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da abokin takararsa a gaban kotun ne saboda cire sunansa da aka yi daga jerin sunayen ’yan takara aka maye gurbinsa da abokin takararsa da ya kayar, Adamu Muhammad Sabon Riga.

Tun farko dai Auwal Seiko, shi ya lashe zaben tsayar da dan takara da kuri’a 13 cikin 14 da aka jefa, amma daga baya da aka fitar da jerin sunayen ’yan takara babu sunansa.

Seiko ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, HN Nwoye, wanda ya shaida wa kotun cewa duk wadanda ake hukumar an aike musu da sammaci a ranar 27 ga watan Oktoba, 2022, amma babu wanda ya halarci zaman kotun na farko.

Nwoye, ya shaida wa kotu cewa yana da tabbacin duk bangarori ukun sun samu sammacin amma har aka shiga kotun a ranar Talata ba wanda ya zo a cikinsu.

Ya roki kotun ta sake ba su damar sake tura musu sammaci, idan kuma ba a same su ba sai a manna a kofar gidajensu ko wajen da suke zama.

Magatakardar kotun ya sanar da kotu cewa dukkan bangarorin sun samu sammacin sai dai dalilin rashin halartar nasu gaban kotu ne ba su sanar ba.

Daga nan sai alkalin kotun, HIO Ufoma, ya amince da rokon lauyan mai karar sannan ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Juma’a 4 ga watan Nuwamba.