Dan takarar Sanatan NNPP a Jigawa, Rabi’u Taura ya rasu

Dan takarar ya rasu bayan ya sha fama da ciwon baya na tsawon lokaci.

Dan takarar Sanatan NNPP a Jigawa, Rabi’u Taura ya rasu

Dan takarar jam’iyyar NNPP na kujerar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma a zaben 2023, Alhaji Rabi’u Isah Taura, ya rasu.

Taura ya rasu ne da safiyar ranar Talata bayan ya sha fama da matsanancin ciwon baya.

Ya yi aiki a matsayin Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa; Kwamishinan Kasa da Safiyo, Kwamishinan Noma da albarkatun Kasa Karkashin Gwamnatin Sule Lamido.

Daga baya ya koma jam’iyyar NNPP tare da uban gidansa, dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Aminu Ibrahim Ringim, wanda a wancan lokaci suka samu sabani da Lamido.

Marigayin ya rasu ya bar mata, ’ya’ya, da jikoki.

Ringim ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba ga iyalinsa kadai ba har ma da jiha da kasa baki daya.

Ya kuma yi addu’ar Allah SWA Ya jikansa, Ya kuma bai wa iyalinsa hakurin jure rashinsa.

Tuni aka yi jana’izarsa a ranar Talata da misalin karfe 10:00 na safe a karamar hukumar Taura.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC