Dan tasi ya kai matarsa da kwartonta kotu

Wani direban tasi mai shekara 26, mai suna Auwalu Zubairu, ya gurfanar da wani mutum Zaharaddeen dahiru da yake zargi da shiga gidansa a Unguwar Kurna tare da lalata da matarsa ’yar shekara 19, mai suna Daraja Abdullahi a gaban Kotun Shari’a ta Fagge da ke Kano.Mijin matar ya bayyana wa kotun cewa ya kama […]

Dan tasi ya kai matarsa da kwartonta kotu
Dan tasi ya kai matarsa da kwartonta kotu

Wani direban tasi mai shekara 26, mai suna Auwalu Zubairu, ya gurfanar da wani mutum Zaharaddeen dahiru da yake zargi da shiga gidansa a Unguwar Kurna tare da lalata da matarsa ’yar shekara 19, mai suna Daraja Abdullahi a gaban Kotun Shari’a ta Fagge da ke Kano.
Mijin matar ya bayyana wa kotun cewa ya kama mutumin ne a cikin gidansa a ranar 31 ga Yulin da ya gabata, bayan ya dawo daga aiki.
Bayanin farko na ’yan sanda da aka gabatar gaban kotun ya nuna cewa a ranar 8 ga watan Agusta ne mijin matar ya kai karar mutanen da ake zargi su biyu ofishin ’yan sanda inda su kuma suka kai maganar gaban kotun. Laifin da ake zargin mutanen biyu da aikatawa, ya saba wa sashi na 187 na dokar shari’a ta jihar.
A yayin da kotu ta tuhumi mutanen da ake zargi, sun amsa laifinsu, kuma kwarton ya kara da cewa abu ne da suka saba aikatawa.
Alkalin kotun, Mai shari’a Abubakar Ayagi, ya dage sauraron karar zuwa lokacin da za a gama bincike a kan lamarin, inda kuma ya ba da umarnin a tsare mutumin da ake zargi a gidan wakafi, ita kuma matar aka bayar da belinta.