dan tasi ya mayar da motarsa dakin karatu a Iran
Wani direban tasi da ke birnin Rasht a kasar Iran ya zuba dimbin littattafai a motarsa don jan ra’ayin fasinjoji ga harkar karatu, inda kafafen yada labarai suka ruwaito yadda motar ta zama tamkar dakin karatu.Sahel Filsoof, direban tasin da ya mayar da motarsa dakin karatu na tafi da gidanka, yana da tabbacin cewa, mutane […]
Wani direban tasi da ke birnin Rasht a kasar Iran ya zuba dimbin littattafai a motarsa don jan ra’ayin fasinjoji ga harkar karatu, inda kafafen yada labarai suka ruwaito yadda motar ta zama tamkar dakin karatu.
Sahel Filsoof, direban tasin da ya mayar da motarsa dakin karatu na tafi da gidanka, yana da tabbacin cewa, mutane za su samu dabarun warware matsalolinsu ta hanyar karanta littattafai, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labgarai na dinhua ya ruwaito.
“Jibge littattafan fannonin ilimi 50 a wannan mota, wadanda suka hada da tsarin tunani da na yara da tarihi, sun sanya mafi yawan masu son hawan motarsa mata ne da samari,” inji shi.
A cewar Filsoof, ya bukaci hukumomin kula da dakin karatu da ke Lardin Arewacin Gilan da su tallafa wannan manufa tasa, sun kuma amince, inda suka bashi dimbin littattafan da suka kara yawan littattafan dakin karatun tafi-da-gidanka.
“Duk sa’adda na samu fasinjan da ya tambaye ni littafin da zai karanta, sai in gane cewa aikina yana yin kyau,” inji shi.