dan uwan Jonathan ya karbi Dala miliyan 40 daga Dasuki – EFCC

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), ta ce ta kama wani tabashin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan mai suna Aziboala Roberts, bisa tuhumarsa da karbar Dala miliyan 40 (kimanin Naira biliyan bakwai da miliyan 840 musayar gwamnati ko biliyan 12 da miliyan 880 a kasuwar bayan fage) daga hannun tsohon Mashawarcin […]

dan uwan Jonathan ya karbi Dala miliyan 40 daga Dasuki – EFCC

g Malam Ibrahim Magu Shugaban Hukumar EFCCHukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), ta ce ta kama wani tabashin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan mai suna Aziboala Roberts, bisa tuhumarsa da karbar Dala miliyan 40 (kimanin Naira biliyan bakwai da miliyan 840 musayar gwamnati ko biliyan 12 da miliyan 880 a kasuwar bayan fage) daga hannun tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Lauyan Hukumar EFCC F.A. Jirbo, wanda ya nuna adawa da bukatar da Robert ya gabatar a gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya yana neman a kare masa ’yancinsa na dan Adam, ya ce wanda ake zargin ya karbi kudin ne daga hannun Sambo Dasuki a watan Satumban shekarar 2014 da niyyar sayo “wasu kayayyakin sadarwa.”
Ya ce wani fom din umarni daga ofishin Dasuki ya nuna cewa an ciro kudin ne daga bankin Citibank N.A. Canada Skuare Canary, da ke kasar Kanada zuwa asusun kamfanin Roberts mai suna Oneplus Holding Limited da ke bankin Zenith Bank Plc.
Ya ce bayanin hada-hadar kudi na asusun bankin Roberts ya kuma nuna a rana 8 ga Disamban 2014, Dasuki ya tura Naira miliyan 650 zuwa asusunsa.
Lauyan ya ce mutum na biyu da ake zargi, Mista Dakoru Atukpa, Babban Daraktan Ayyuka na Oneplus, ya ce sun yi amfani da kudin ne wajen karfafa dabarun samar da zaman lafiya da hana fasa bututun man fetur da kuma saukaka samar da mai ta hanyar aikin gas na NNPC LNG a garuruwan Olokola da Brass a shekarar 2014.
Sai dai lauyansu, Chris Uche (SAN), ya ce gazawar Hukumar EFCC ta saki wanda yake karewa, “wani babban raini ne da rashin biyayya ga umarnin kotu.”