Dan wasan kwallon kafa ya kashe kocinsa a Kano

Ana tuhumar wani dan wasan kwallon kafa mai suna Salisu Muhammad mai shekara 18, da laifin dabawa kocinsa wuka akan gardamar kwallon kafa. Kocin mai suna Mujitapha Musa an kashe shi ne a rukunin gidaje na unguwar Yakasai dake karamar hukumar Kano Municipal a jihar Kano. Kocin ya rasu ne a babban asibitin Murtala Muhammad […]

Dan wasan kwallon kafa ya kashe kocinsa a Kano

Ana tuhumar wani dan wasan kwallon kafa mai suna Salisu Muhammad mai shekara 18, da laifin dabawa kocinsa wuka akan gardamar kwallon kafa.

Kocin mai suna Mujitapha Musa an kashe shi ne a rukunin gidaje na unguwar Yakasai dake karamar hukumar Kano Municipal a jihar Kano. Kocin ya rasu ne a babban asibitin Murtala Muhammad sakamakon raunin da ya samu a kirjinsa.

Kakakin hukumar ‘yan sanda DSP Haruna Abdullahi ya ce, a  yanzu haka jami’an tsaro sun kama Salisu Muhammad da wukar da ya yi amfani da ita wajen dabawa kocinsa tare da wani da ya jiwa rauni mai suna Suleiman Muhammed.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno