Dan wasan Chess da ake zargi da magudi ya yi biris da martanin mutane
Wani fitaccen dan wasan Chess mai shekaru 19 Hans Niemann da ake zargi da aikata magudi a nasarar da ya samu a wasanninsa na baya, ya yi biris da ce-ce-ku-cen da ake yi kan lamarin. A ranar Talata ne dai wani bincike na Chess.com ya yi ikirarin cewa akwai yiwuwar Hans Niemann ya aikata magudi […]
Wani fitaccen dan wasan Chess mai shekaru 19 Hans Niemann da ake zargi da aikata magudi a nasarar da ya samu a wasanninsa na baya, ya yi biris da ce-ce-ku-cen da ake yi kan lamarin.
A ranar Talata ne dai wani bincike na Chess.com ya yi ikirarin cewa akwai yiwuwar Hans Niemann ya aikata magudi a fiye da wasanni 100 na yanar gizo.
- WHO ta soma bincike kan maganin Indiya da ya kashe yara 66 a Gambia
- Kamfanin Google Cloud zai bude ofishinsa na farko a Afirka
Da yake tsokaci bayan ya yi magana karon farko kan zargin cikin kusan wata guda, matashin ya ce ba gudu ba ja da baya a wasannin nasa.
Ko a baya ma zakaran duniya na wasan mai suna Magnus Carlsen ya zargi matashin da aikata magudi a karawarsu, sai dai matashin ya yi biris da batun.
A ganawarsa da manema labarai bayan karawarsa da zakaran duniya da ke tashe, Christopher Yoo mai shekaru 15, an tambayi Niemann game da badakalar, inda nan ma ya ki cewa komai kan lamarin.
“Abinda kawai zan ce shi ne da na samu ta yanzu somin tabi ne, kuma zan ci gaba da buga wasanni mafi kyauwua gaba, ba tare da la’akari da abinda mutane ke cewa ba.”
“Sauran na bar ku da tunaninku kawai.”
Daga nan ne kuma Niemann ya yanke hirar ta sa da ba ta wuce ta dakika 60.