dan wasan Hausa Nura M.C. ya zama ango

A ranar Asabar din da ta gabata ce aka daura auren fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Nuraddin Muhammad Usman wanda aka fi sani da lakanin Nura MC Khan da amaryarsa Abida Mustapha Isma’ila.An daura auren ne a masallacin Salamat da ke Unguwar Mu’azu a yankin karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna.Rahotanni sun bayyana cewa an […]

dan wasan Hausa Nura M.C. ya zama ango
dan wasan Hausa Nura M.C. ya zama ango

Ango, Nura MC (a dama) da amaryarsa Abida (a hagu) da kuma jarumi Abdulaziz M Sharif (daga baya)A ranar Asabar din da ta gabata ce aka daura auren fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Nuraddin Muhammad Usman wanda aka fi sani da lakanin Nura MC Khan da amaryarsa Abida Mustapha Isma’ila.
An daura auren ne a masallacin Salamat da ke Unguwar Mu’azu a yankin karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da shagulgula da dama don murnar auren, inda aka karkare da walimar bikin a dandalin shakatawa na Gamji Gate Kaduna.
dimbin abokan sana’arsa ne suka halarci daurin auren tare da shagalin bikin, wadanda suka hada da jarumai kamar su Adam A Zango da Abbas Sadik da Abdulaziz M. Sharif da kuma mawaka kamar su Umar danhausa da Umar M. Sharif da Malam Yahaya Makaho da sauransu. Har ila yau, bikin ya samu halartar editan Jaridar Leadership Hausa, Al-Amin Ciroma.
Nura ya bayar da gudunmawa mai yawa a masana’antar fina-finan Hausa a ’yan shekarun nan. Ya kuma fito a fina-finai kamar su Sai Wata Rana da Kudi A Duhu da Bissalam da Kaicona da Hasken Zuci da Alkawari da Adamsy  da kuma Barti Ko Marti da sauransu.