dana mai tabin hankali ne ba shi ya kai wa Buhari hari ba –Mahaifiyarsa
Malama Zubaida Yusuf ita ce mahaifiyar matashin da aka kama cikin tufafin mata a ranar da aka kai wa tsohon Shugaban kasa Janar Buhari harin Bam a kusa da tashar motar Kawo Kaduna. A wannan zantawar da Aminiya ta karyata zargin da ake wa danta cewa shi ne ya jefa wa Buhari bam. Domin a […]

Malama Zubaida Yusuf ita ce mahaifiyar matashin da aka kama cikin tufafin mata a ranar da aka kai wa tsohon Shugaban kasa Janar Buhari harin Bam a kusa da tashar motar Kawo Kaduna. A wannan zantawar da Aminiya ta karyata zargin da ake wa danta cewa shi ne ya jefa wa Buhari bam. Domin a cewarta yana fama da rashin lafiya ne ta shafar aljanu wanda ke sanya shi sanya kayan mata. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me za ki ce game da zargin da ake yi wa danki na yunkurin halaka tsohon Shugaban kasa, Janar Buhari?
Zubaida: Da farko dai zan so Janar Buhari da sauran ‘yan Najeria su sani cewa dana Mansir ba dan ta’adda bane. Ba shi da zuciyar aikata irin wannan ta’asa. Matsalarsa dai ita ce yana da matsalarashin lafiya ko aljannu da ke damunsa. Abin da ke faruwa a kasar nan a yanzu babu wata uwa da za ta so a ce danta na cikin masu aikata irin wannan ta’asa. Wannan yasa na soma kuka a lokacin da na samu labarin abin da ya faru domin abin da ban mamaki. Kuma dukkanmu da ke gidan nan tare da ‘yan hayan da ke cikin gidan nan duk mun shiga damuwa. Mijina mutum ne mai addini kuma mutumin kirki kafin Allah Ya yi masa rasuwa. Baya ga wannan rashin lafiya ko aljanu da ke damun Mansir, ba ni da wata damuwa dangane da tarbiyar ‘ya’yana, saboda sun samu tarbiya ta gari.
Aminiya: Ko za ki fada mana abin da aka ce miki ya faru a wannan rana da aka kama shi?
Zubaida: Ina gida lokacin da na samu labarin cewa wai matasa sun yi masa duka har sai da suka kashe shi a Kawo saboda wai suna zarginsa da kai harin bam. Amma daga baya sai na sake samun labari kuma Sojoji sun cece shi sun kai shi asibitin 44 domin duba lafiyarsa. A wannan rana ba ya gida a daidai lokacin da aka kai harin, ni kuma da na kira shi domin sanin inda yake sai ya ce da ni yana Unguwar Sarki. Na umurce shi da ya dawo gida ta Hayin banki, amma sai ya ce da ni wai za shi inda aka kai harin bam din a Kawo domin gane wa idonsa abin da ya faru. A wajen ne wani ya ganshi a cikin kayan mata har ya fada wa sauran mutanen da ke wajen cewa ga namiji cikin kayan mata. Nan take kuma sai matasa suka hau shi da duka a bisa zargin wai yana da hannu a harin da aka kai.
Aminiya: Meye ainihin dalilin da ya sa Mansir ya sanya tufafin mata a wannan rana tun da ba kullum yake sanyawa ba ko?
Zubaida: Kamar yadda na fada maka ne, yana tare da aljanu da ke damunsa. Babban matsalar da ke damunsa ke nan, wanda a kusan kowane lokaci suke sa shi sanya kayan mata kuma ya rika halayya irin ta marasa hankali. Duk wani mazaunin Mando ya sanshi da wannan dabi’a. Mafi yawan lokuta yana sanya kayan maza ne a gida, amma da zarar ya fita unguwa sai ya shiga kango ko wani waje ya canza kayansa zuwa na mata. Wani lokaci yana sanya kayan matan ne a cikin jakarsa na hannu. Mun sha daukarsa zuwa gidan Sarki inda ake yi masa bulala da nufin fitar masa da wadannan aljanu, saboda ya bar wannan dabi’a amma ina, abin ya ki ci ya ki cinyewa.
Aminiya: Mutane sun ce wai an same shi da bam a cikin jakar da ke hannunsa, ko gaskiya ne?
Zubaida: karya ne, duk wanda ya fadi haka sharri ne, kuma a ranar alkiyama sai Allah Ya yi mana hisabi dukkanmu. A ina ya samu bam? Waye kuma zai ba shi bam? Abin da yake yawan dauka a cikin jakarsa sune wayoyinsa da kuma kayansa. Kuma abin da kawai ke nan aka gani a jakansa. Inda yarona dan ta’adda ne da mutanen da ke zaune a gidan mahaifinsa da kuma makwabta babu yadda za a yi su zauna lafiya. Mu kanmu da ke a gidannan muna Allah wadai da abin da ke faruwa, kuma a kullum addu’a muke yi na zaman lafiya. Ina kira ga gwamnati da sauran jama’a da su zo layin Aminu Kano a Mando su tambayi waye Mansir Yusuf, duk kusan an sanshi da wannan matsalar, domin ya yi shekaru yana fama da wannan rashin lafiya. Wadannan aljanu su ke hana shi yin aikin komai, amma dai ba ya cikin masu aikata mugun hali.
Aminiya: Baya ga ‘yan gidanku da makwabta waye kuma ya san Mansir na fama da wannan rashin lafiya?
Zubaida: Kusan duk wanda ya sanshi a Mando yana da labarin rashin lafiyarsa. Sarkin unguwar ya sani, masu hayan a cikin gidanmu sun sani, mazauna kan titin mu sun sani. Kai amma taba shirya wani labari a kansa a gidan Talibijin na DITb a matsayinsa na yaro mai sanya kayan mata. Idan ana shakku sai a je gidan Talibijin na DITb a tambaya.
Aminiya: Wa yake ba shi kayan mata?
Zubaida: Kayan kanwarsa yake kwashewa. Idan ya kwashe sai ya gudu ya je ya canza a kan hanya, sai ya saka kayansa a cikin jakarsa na hannu. Abin da yake yi ke nan.
Aminiya: Shin ko jami’an tsaro sun zo nan gidan naku domin gudanar da bincike?
Zubaida: A’a ba su zo ba.
Aminiya: Me ya hana jami’an tsaro sako shi, tunda ba su kama shi da wani laifi ba, kuma gashi kin ce ba su zo nan gidan ba domin gudanar da bincike?
Zubaida: Yana asibiti yana karbar magani saboda ya sha duka a hannun mutane. Suna lura da lafiyarsa ne tukun.
Aminiya: Kina ganin za su sake shi idan ya warke?
Zubaida: Gaskiya ban sani ba; domin har yanzu yana wajensu. Amma tunda ba su same shi da wani mugun abu ba ya kamata su sake shi don Allah.
Aminiya: Ko kin ziyarce shi a asibitin?
Zubaida: Ban je ba har yanzu, amma dai zan je. daya daga cikin yayyensa na wajensa tun lokacin da abin ya faru. Da farko dai mutane suna ta fadin cewa wai kada mu je saboda za a kama mu.
Aminiya: An kama yayan nasa da ke wajensa?
Zubaida: A’a ba a kama shi ba.
Shaidar da mutane suka bayar game da shi
Da wakilinmu ya ziyarce gidan Sarkin Unguwar Mando domin jin ta bakinsa game da labarin rashin lafiyar Mansir sai aka fada masa cewa sarki ba shi da lafiya, amma dai wani daga cikin ‘yan gidan Sarkin da ya ki yarda ya ambaci sunansa domin ba a bashi iznin yin magana da ‘yan jarida ba ya tabbatar wa Aminiya cewa maganar mahaifiyar Mansir gaskiya ne, inda ya ce hakika yaron yana fama da rashin lafiya wanda ke sanya shi sanya tufafin mata. “ An dade ana kawo shi nan fada domin sama masa taimako. Mun sha bai wa ‘yan’uwansa shawara a kan abin da ya kamata su yi a kan rashin lafiyarsa, wanda muna ganin kamar sun fara aiwatarwa,” inji shi.
Shi ma Ibrahim Yusuf, wanda dan uwa ne ga Mansir, ya bayyana cewa rashin lafiyar da kanensa ke fama da shi yana da alaka da aljanu, domin ba ya iya yin kowane irin aiki, shi dai a kullum kawai abin da yake son sakawa shi ne kayan mata. Su kuma mutanen da ba su san shi ba sai su rika daukarsa da wata manufa.
Wani mazaunin Kawo inda bam ya din ya tashi, mai suna Sirajo Suleiman, ya tabbatar wa Aminiya cewa, lokacin da aka kama matashin da aka duba jakar da ke hannunsa ba a ga komai ba sai wayoyin hannunsa, sai wadansu kayan sawa.
Shi kuwa Malam Sani, wani mai sayar da tayoyi a kusa da inda bam din ya tashi cewa ya yi,” Ni dai gaskiya ko da na ganshi ya yi min kama ne da dandaudu, kuma saboda yana sanye da tufafin mata sai na dauka yana da tabin hankali,” inji shi.