Dandalin Maza da Mata na Rediyon Unity Jos ya koya wa matasa 150 sana’o’i

kungiyar Dandalin Maza da Mata ta gidan Rediyon Unity da ke Jos fadar Jihar Filato, ta shirya gagarumin taron kaddamar da matasa 150 da ta koya wa sana’o’i daban-daban, a karshen makon jiya. Da yake jawabi a wajen taron wani jami’in ’yan sanda mai taimaka wa al’umma, Alhaji Abubakar Aljuma Sadik [Sadik Plaza] ya yi […]

Dandalin Maza da Mata na Rediyon Unity Jos ya koya wa matasa 150 sana’o’i

kungiyar Dandalin Maza da Mata ta gidan Rediyon Unity da ke Jos fadar Jihar Filato, ta shirya gagarumin taron kaddamar da matasa 150 da ta koya wa sana’o’i daban-daban, a karshen makon jiya.

Da yake jawabi a wajen taron wani jami’in ’yan sanda mai taimaka wa al’umma, Alhaji Abubakar Aljuma Sadik [Sadik Plaza] ya yi kira ga jama’a musamman masu hali da su rika tallafa wa marasa galihu.

Sannan ya yi kira ga wadanda suka amfana da wannan shiri na koyar da sana’o’i su mayar da hankali don sun ci gajiyar sana’o’in da aka koya musu. 

Kuma ya yi kira ga al’ummar Najeriya su guji yada jita-jita, domin jita-jita ne ke kawo rashin kwanciyar hankali a cikin al’umma. 

A jawabin, Shugaban kungiyar kuma mai shiryawa da gabatar da shirin Dandalin Maza da Mata a gidan Rediyon Unity FM da ke Jos, Malam Nazifi Abdullahi ya ce sun shirya taron ne domin kaddamar da matasa 150 da suka koya wa sana’o’i daban-daban da suka hada da dinki da daukar hoto da aiki da na’urar kwamfuta da gyaran gashi da aski da sauransu.

Ya ce sun kafa kungiyar ce bayan fito da shirin Dandalin Maza da Mata da yake mayar da hankali wajen sasanta tsakanin ma’aurata da rikicin gado ta hanyar  kiran wadanda irin wadannan al’amura suka shafa su zauna da su su sasanta su. 

“Don haka sai muka ga ya dace mu fito da wata kafa da za mu rika tallafa wa matasa suna samun sana’a domin su dogara da kansu. Don haka muka kafa kungiyar ta Dandalin Maza da Mata. Kuma bayan haka muna zuwa gidajen marayu da gajiyayyu domin mu tallafa musu. Babban burinmu kan wannan shiri shi ne mu ga cewa mun kori zaman banza a tsakanin matasanmu da kawo zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al’ummar Najeriya baki daya,” inji shi.

Taron ya samu halartar Shugaban Gidan Rediyon Unity FM, Jos Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu Nakande da Janar Manajan gidan Rediyon Hajiya Larai Baba da sauran manyan baki da kungiyoyi daga wurare daban-daban.