Dandalin Waiwaye ya yi taron bunkasa harshen Hausa
A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar Dandalin Waiwaye ta gudanar da taron bita na yini daya ga ’ya’yanta da kuma ’yan jarida game da yadda za a bunkasa harshen Hausa tare da farfado da al’adun Hausawa. A jawabinsa na maraba, Shugaban Dandalin Malam Ibrahim Muhammad Mandawari ya tabo tarihin kungiyar tasu inda […]
A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar Dandalin Waiwaye ta gudanar da taron bita na yini daya ga ’ya’yanta da kuma ’yan jarida game da yadda za a bunkasa harshen Hausa tare da farfado da al’adun Hausawa.
A jawabinsa na maraba, Shugaban Dandalin Malam Ibrahim Muhammad Mandawari ya tabo tarihin kungiyar tasu inda ya ce kungiyar ta samo asali ne daga wani shiri da ake gabatarwa a gidan Rediyon Freedom a Kano, inda shi a matsayinsa na mai gabatar da shirin da masu sauraronsa suka hadu suka kafa shi. “Ni da masu sauraren shirin ‘Waiwaye’ mukan hadu a shafin sadarwa na Whatsapp, inda muke tattuna muhimman abubuwan da suka danganci yadda za a ciyar da harshen Hausa gaba da sauransu. Haka kuma haduwarmu a dandalin ta haifar mana da zumunci sosai, inda mukan taya junanmu murna a lokacin wani abu na farin ciki ko bakin ciki a lokutan da suka yi rashi da suaransu.”
Mandawari ya kara da cewa: “Duba da yadda harshen Hausa yake da muhimmanci a wurinmu muka ga dacewar yin wannan taro wanda shi ne irinsa na biyu. Mun gabatar da na farko a bara a gidan Rediyon Freedom. A gaskiyar Magana, harshen Hausa ba zai samu bunkasa yadda ake fata ba har sai Hausawan da kansu sun dabbaka harshen ta yadda za su zama masu alfahari da shi a ko’ina a duniya.”
Ya bayyana cewa a kokarin Dandalin na ganin harshen Huasa ya bunkasa, yana kan shirye-shiryen sanya gasa tsakanin marubuta wakokin Hausa. “Baya ga sanya gasa da Dandalin zai rika yi duk shekara tsakanin marubuta wakoki, har ila yau dandalin yana tunanin samar da kafar sadarwa tasa ta kansa a intanet, ta yadda za a iya samun su kai tsaye a ko’ina a fadin duniya. Har’ila yau yana da burin ganin ya wallafa ire-iren makalolin da ake gabatarwa a irin wadannan tarurruka a matsayin littafi don amfanin jama’a” Inji shi.
A karshe Mandawari ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta rika daukar nauyin wasu shirye-shirye na bunkasa Harshen Hausa, musamman a lokutan da manyan makarantun jihar ke gabatar da makon Hausa.
Shi ma a jawabinsa shugaban taron, malami a Sashen Tarihi na Jami’ar Bayero Kano Farfesa dahiru Yahaya ya bayyana cewa harshen Hausa harshe ne da tun farko yake da wayewa, idan aka yi la’akari da dimbin kalmomi da yake da shi. “Sai dai akwai bukatar masu amfani da shi su kara bunkasa shi ta hanyar ciyar da shi gaba. Haka kuma su ma ’yan jarida a nasu bangaren, suna da rawar takawa wajen bunkasa harshen ko kuma nakasa shi idan aka yi la’akari da dimbin jama’ar da ke sauraron su ko karanta su” Inji shi.
Manyan malamai da manazarta harshen Hausa daga Jami’ar Bayero Kano da suka hada da Farfesa dahiru Yahaya da Farfesa Isa Muktar da Dakta Aliyu Mu’azu da Dokta Murtala Garba Yakasai da Dokta Ibrahim Satatima da sauransu, sun gabatar da makaloli game da abin da ya shafi tarihin asalin Hausawa da yadda Hausawa ke aure jiya da yau da sauransu.