Dangin wadanni 11 mafi gajarta a Duniya
Allah ne Ya halicce mu a yanayin da yake son ganinmu.
An haifi wata wada mai suna Anne Marie a cikin danginsu su 11, amma ta kasance mafi kankanta a duk cikin ’yan uwanta.
Ta kasance karama ga gajarta a cikin wadanda aka haifa tun suna kanana, amma daga haihuwarta iyayensu suka ci gaba da haihuwar masu kankantar jiki irin na Anne.
- Mazauna Saudiyya 60,000 ne kadai za su yi aikin Hajjin bana
- Mun cire ’yan Najeriya 10.5m daga kangin talauci —Buhari
A cikin wani sabon bidiyo, dangin iyalan mafiya gajarta a duniya, da jama’a da dama suke bayyana su a matsayin gajerun duniya da kuma yadda kamanninsu ke zama kamar wata sabuwar halitta a cikin mutane.
Wani shirin bidiyo da Afrimax ya wallafa a kafar Youtube, ya dauki rahoton iyalan da aka ce su ne mafi gajarta a duniya.
Mahaifiyarsu, Anne Marie wacce ba ta san ainihin shekarunta ba, ta ce iyayenta sun haifi ’ya’ya 11 amma sai ta zama ita ce mafi kankanta a cikinsu.
Dan Anne mai suna Katihabwa, ya ce ya gaji da shirin yin aure, amma sai auren ya wargaje daga wajen matan da yake kokarin aura, iyayensa sun haife su biyar, uku daga ciki na da tsawo sai biyu kuma gajeru ne.
Katihabwa wanda jarumin mutum ne ya bayyana yadda suke shan azaba da izgili daga wajen mutane amma abin da suka sa a gaba shi ne ai su ma Allah ne Ya halicce su a yanayin da yake son ganinsu.
Daya daga cikin ’ya’yan Anne mai suna, A’isha ta bayyana cewa an haife ta ce da tsayinta, amma abin mamaki bayan wasu shekaru sai ta fara zama gajera.
Khadidja daya daga cikin ’ya’yan Anne ta yi tir da yadda iyaye suke hana yaransu zuwa ganinsu ko mu’amala da su, amma ta ce sun riga sun saba da hakan.