Dangote da ’yan Mafiyar Man Fetur
Da galibinmuu suka tuno da korafin da Babban Shugaban Matatar kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya yi cewa manyan kamfanonin mai na duniya da suke Nijeriya suna hana shi danyen mai sai muka ji gwiwarmu ta yi sanyi.
Lokacin da muka ziyarci Matatar Dangote da ke yankin Lekki a Legas a makon jiya, abubuwan da muka gani a matatar da kamfanin takinsa da tashar jiragen ruwa da ya gina, sun ba mu karfin gwiwar cewa kasar nan za ta dawo cikin hayyacinta ta dogara da kanta a fannoni da dama.
To amma da galibinmuu suka tuno da korafin da Babban Shugaban Matatar kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya yi cewa manyan kamfanonin mai na duniya da suke Nijeriya suna hana shi danyen mai sai muka ji gwiwarmu ta yi sanyi.
Ni a lokacin na tuno da abubuwa biyu da suka faru a kan Matatar Mai ta Kaduna da suka nuna cewa ’yan Mafiyar Man Fetur za su ci gaba da yin duk abin da za su iya, don kassara duk wani yunkuri na ganin Nijeriya ta dogara da kanta wajen samar da man fetur.
Na daya ya faru ne a zamanin Janar Abacha, inda aka ce Matatar Kaduna na bukatar wasu miliyoyin daloli don sayo wani bangare na kayan aiki da ya lalace a cikinta, amma sai shugaban matatar na lokacin ya ce, in aka ba shi kashi 20 na kudin zai je Kamfanin karafa na Ajaokuta a yi bangaren ya zo ya hada.
An ce Janar Abacha ya ba shi kudin ya je aka yi bangaren ya zo ya hada, matatar ta fara aiki.
- Gwamnati ta soma ɗaukar mataki kan fim ɗin wulaƙanta Hijabi
- Shugaban Gabon ya gayyaci Dangote ya kafa masana’antun taki da siminti a kasarsa
- Matatar Dangote: Ku zo ku saya ku yi yadda kuka ga dama —Dangote ga NNPCL
Amma ’yan Mafiyar Fetur suna ganin haka, suka sa aka yi masa canjin wurin aiki zuwa Kudu.
Sai zamanin marigayi Shugaba Umaru ’Yar’aduwa wanda aka ce ya kashe Dala miliyan 50 wajen gyara Matatar Kaduna, amma ba ta fi kwana 100 ba ta sake lalacewa.
Wannan ya sa ’Yar’aduwa ya ce zai sayar da matatu da rijiyoyin mai, amma kungiyoyin kwadago da na jama’a da kafafen watsa labarai suka yi masa ca.
Hakan ya sa ya yanke shawarar gwamnati ta shiga harkar mai ya ce a giggina manyan gidajen sayar da mai a jihohi da kananan hukumomi, kuma ya ce gwamnati da ’yan kasuwar mai su hadu a kasuwa kowa ya sayar yadda yake so.
A karshe dai mafarkinsa bai cika ba, gwamnatocin da suka biyo baya ba su cika wannan buri ba, kila saboda ’yan Mafiyar Fetur sun fi karfinsu.
Wani makwabcina a Unguwar Badarawa, Kaduna, da ke harkar kananzir a matatar ya taba fada min cewa lokacin da ’Yar’aduwa ya gyara matatar wani direban tanka ya yi addu’ar Allah Ya sa ta dade tana aiki, amma mai gidansa na ji ya ce, in ta dade tana aiki don abin kazarka a ina za ka ci abinci?
Kuma ya ce a waccan shekara, mutum 200 aka tura Umarah su je su roki Allah matatar ta lalace!
Da irin wannan tunani na rika ganin lallai Alhaji Aliko Dangote ya yi babbar kasada, kuma akwai jan aiki a gabansa da mu kanmu al’ummar kasa, domin ’yan Mafiyar Fetur ba za su kwanta suna gani ana kashe musu hanyar da suke samu ba.
Wadannan ’yan Mafiyar Fetur su ne suke karkatar da kudin tallafin mai, kuma saboda sun fi karfin gwamnati, maimakon a hukunta su, sai dai a kara wa talaka wahala da sunan janye tallafi.
Wadannan ’yan Mafiyar Fetur su ne suka jawo aka daure tsohon dan Majalisar Wakilai daga Kano, Faruk Lawan, yayin da suke yawo a ciki da wajen Nijeriya ba tare da an hukunta su ba.
Wani soja da ya yi aiki a Legas kuma ya yi aikin tabbatar da zaman lafiya a kasashen Saliyo da Laberiya, ya taba shaida min cewa sun sha ganin man fetur din Nijeriya da ake kawowa bakin tekun Nijeriya a tantance cewa an kawo sai a karkatar da shi zuwa Saliyo ko Laberiya a rika sayarwa a can a kan Naira 400 kowace lita maimakon Naira 97da ake sayarwa a Nijeriya a lokacin
Su wane ne masu yin haka ’yan Mafiyar Fetur wadanda a yanzu suka taso Matatar Dangote a gaba suna ta yi masa zarge-zarge na raina wa jama’a hankali.
Sun ce mansa ba ya da karko amma sai suka tuna an kai shi Amurka an sayar. Sun dawo suna cewa wai Alhaji Aliko Dangote na son yin babakere ne ya hana shigo da mai daga waje, wai matatarsa ba ta wuce kashi 45 ba.
An ce Matatar Fatakwal na daf da fara tace mai, ta Kaduna ma haka, to, abin tambaya don me za a ci gaba da ba da lasisin shigo da mai in ma ba a son Dangoten?
Shin ina kamfanoni sama da 40 da aka ba su lasisin yin matatu suke?
Mutanen nan suna nuna wa duniya ce cewa ba su da kishin kasa kwata-kwata.
Koda Matatar Dangote kadai take aiki, tunda dai babu wata a Nijeriya kuma za ta iya wadata kasar da mai, don me za a bayar da lasisin shigo da tataccen mai daga waje?
A yayin ziyarar tamu Dangote ya shaida mana cewa, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya karafafa masa gwiwa cewa maimakon shigo da kayayyaki daga kasashen waje me zai hana ya kafa masana’anta ya rika sarrafa kayayyakin a nan cikin gida.
Ya ce wannan ne ya sa ya sayar da gidansa a Amurka da Ingila ya zuba jarin wajen kafa kamfanoni.
Alhaji Aliko Dangote ya ce, yana da akidar cewa duk kasar da ta dogara da shigo da kaya cikinta, tana shigo da talauci ne zuwa kasarta yayin da take raya aiki a kasashen waje.
Ya tabo batutuwa da dama inda ya ce akwai lokacin da ya rika nadamar aikin gina matatar, saboda zame kafa da cin dunduniya da zagon kasa da ya rika cin karo da su.
Ya ce ya ci gaba da aikin ne kawai saboda a lokacin ya iske kansa tamkar a tsakiyar teku ta yadda ko dai ya ci gaba da iyo har ya fito ko ya nutse.
Dangote ya kuma koka cewa manyan kamfanonin mai na duniya sun ki sayar masa da danyen mai abin da ke tilasta shi zuwa kasashen waje ya sayo.
Kuma ya yi korafin cewa kason gwamnati a matatar bai wuce 7.2 ba, duk da cewa ta shelanta wa duniya cewa za ta sayi kaso 20. kila fadin hakan ya sa a ranar Alhamis din makon jiya Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta kasa (NMDPRA), ta fito tana cewa wai ba ta ba Matatar Dangote lasisin fara aiki a kasar nan ba.
Babban Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ne ya shaida wa duniya haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban kasa a Abuja.
Ya ce da’awar cewa ana yin zagon kasa ga Matatar Dangote ta hana ta danyen mai daga manyan kamfanonin duniya ba gaskiya ba ce.
Ya ce har yanzu matatar tana matakin jiran kaddamarwa ce kuma ba a ba ta lasisi ba.
Take Alhaji Aliko Dangote ya mayar da martani cewa damawani abokinsa da ya fara zuba jari a kasar waje shekara hudu da suka gabata ya fara yi masa dariya kan kwan-gaba-kwan-bayan da gwamnati ke yi a bayan nan kan matatar.
A tattaunawa da jaridar intanet ta PREMIUM TIMES, Dangote ya bayyana yadda ya yi kokarin nuna wa abokin nasa cewa ya yi kokarin fifita kishin Nijeriya, amma ga shi yanzu na yi masa dariya.
“A shekara hudu da suka gabata daya daga cikin abokaina mai dukiya, ya fara zuba jari a kasar waje.
“Na nuna masa hakan bai dace ba, inda na bukaci ya sake tunani don amfanin kasarsa.
“Ya ce ya dauki matakin ne saboda yawan canja tsare-tsare da zame kafar masu son kai.
“Wannan aboki ya fara zolayata a ’yan kwanakin nan, yana cewa, ya gargade ni, ga shi abin da ya fada na tabbata,” in ji Dangote.
Ya ce ya zuba jari a aikin ne don taimakawa a magance wata babbar matsala a kasar nan inda ya yi mamakin dalilin da wasu mutane ke kokarin karya shi.
“Kamar yadda kuka sani yanzu shekarata 67, nan da kasa da shekara uku zan cika shekara 70. Rayuwar da ta rage min kadan ce. Ba zan dauki matatar ko wata dukiya zuwa kabarina ba. Duk abin da na yi na yi ne don amfanin kasata.
“Muna fuskantar matsalar mai tun shekarun 1970.
“Wannan matata za ta iya magance matsalar, amma sai ga shi wasu mutane ba su jin dadin cewa ni nake aikin. Don haka a shirye nake in sayar, idan Kamfanin NNPC zai saya daga gare ni ya gudanar da matatar. Akalla kasar nan za ta samu ingantaccen mai kuma ta samar da aikin yi,” in ji shi.
Matatar Dangote wadda za ta iya tace mai ganga dubu 650 a kullum ta fara aiki ne a karshen shekarar 2023 bayan daukar shekaru ana gina ta, kuma ta lashe Dala biliyan 19, sama da ninkin yadda aka shirya za ta ci, wadda za ta iya samar da kudin musaya ga kasar nan da kimanin kashi 30 cikin 100, sai dai kash, yanzu ’yan Mafiyar Fetur na son ganin bayanta!
Wannan matsala fa kasa take kassarawa ba Dangote kawai ba. Kada a yarda a bari ’yan Mafiyar Fetur su yi nasara.