dangote ya aika da tirela 106 don ciyar da ’yan gudun hijira a azumi
Akalla ’yan gudun hijira dubu 30 ne da iyalansu za su fara cin gajiyar tallafin Gidauniyar dangote na ciyarwar azumi, a karon farko a wasu daga cikin sansanonin ’yan gudun hijira da ke Jihar Borno a daidai lokacin da jerin gwanon motoci dauke da kayan abinci suka fara isa Maiduguri don fara gudanar da shirin.Babbar […]
Akalla ’yan gudun hijira dubu 30 ne da iyalansu za su fara cin gajiyar tallafin Gidauniyar dangote na ciyarwar azumi, a karon farko a wasu daga cikin sansanonin ’yan gudun hijira da ke Jihar Borno a daidai lokacin da jerin gwanon motoci dauke da kayan abinci suka fara isa Maiduguri don fara gudanar da shirin.
Babbar Manaja a Gidauniyar Hajiya Zouwaira Yousufu, ta bayyana haka bayan da ta mika wasu daga cikin kayayyakin a sansanin ’yan gudun hijra na Bakasi da ke garin Maiduguri.
Hajiya Zouwaira Yusufu, ta ce “A bisa alkawarin da Alhaji Aliko dangote yayi a watan jiya na cewa zai dauki nauyin ciyar da daukacin ’yan gudun hijirar to yanzu mun zo cika alkawari ne mun kuma zo da manyan motocin daukar kaya guda 106, dauke da buhunan shinkafa da taliya da Semobita da sukari da sauransu, kuma kayan abincin ba su da nasaba da kudin da ya yi alkawarin bayarwa na Naira biliyan biyu, domin wancan kudi ana sa ran za a kashe su ne a bangarorin ilimi da kiwon lafiya da kula da mata don haka wannan abinci daban, wancan kudi daban.”
Wani dan gudun hijira mai suna Malam Bukar wanda ya fito daga karamar Hukumar Guzamala ya ce agajin zai taimaka musu matuka wajen ciyar da iyalansu a wannan lokaci na azumi, saboda sun gode wa Alhaji Aliko dangote tare da yi masa addu’ar Allah Ya saka masa da alheri. Ya shaida wa wakilinmu cewa: “Matana biyu da ’ya’ya 15, a da muna samun wahala kafin mu samu abinci a yini duk da cewa muna cikin sansanin gudun hijira, gwamnati na daukar nauyinmu, to amma wasu ne kawai ke amfana da shirin
ga shi kuma mun shiga azumi a gaskiya ya taimaka mana, an ba ni kayayyakin abinci, shinkafa da sukari da taliya da semobita da sauransu, kuma zai kwana mana biyu,” inji shi.
Ita kuwa Hajiya Falmata cewa ta yi, “Ai mu yau take Sallah domin abin da muke nema ido rufe da ya zama mana mai kamshin turaren dan goma sai ga shi yau mun same shi kuma zai dauke mu na wani lokaci mai tsawo. Mu da ’ya’yanmu mun huta da wahalar neman abinci ta hanyar roko ko bara, ko yadda gwamnati ta ke ba mu, amma wadansu suke danne mana su bar mu da yunwa. Yanzu dangote ya ba mu hannu-da-hannu, Allah Ya saka masa da alheri,” inji ta.