Dangote ya ba da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda rikicin Mambila ya shafa
Shugaban Rukunonin Kamfanin dangote, Alhaji Aliko dangote ya ba da tallafin Naira miliyan 50 ga al’ummar Fulani da rikicin Mambila ya shafa a Jihar Taraba.Tallafin ya zo ne a daidai da lokacin da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta fara raba kayan abinci da magunguna ga ’yan gudun hijirar. Alhaji Aliko Dangote […]

Shugaban Rukunonin Kamfanin dangote, Alhaji Aliko dangote ya ba da tallafin Naira miliyan 50 ga al’ummar Fulani da rikicin Mambila ya shafa a Jihar Taraba.Tallafin ya zo ne a daidai da lokacin da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta fara raba kayan abinci da magunguna ga ’yan gudun hijirar.
Alhaji Aliko Dangote wanda ya ziyarci Gwamnan Jihar Taraba, Mista Darius Ishaku a Jalingo ya yi ta’aziyya da jaje ga gwamnati da al’ummar jihar game da asarar rayuka da dokiyoyi da rigimar ta jawo.
Ya ce akwai bukatar a’lummar kasar nan sun zauna lafiya da juna domin ta haka ne kawai za a samu ci gaba ta fuskarkar tattalin arziki da zamantakewa. Ya yi fatan hakan ba zai sake aukuwa a jihar ba, musamman ganin yadda jihar ke da dimbin albarkatun da za su iya kawo ci gaba mai amfani ga al’ummar jihar da kasa baki daya. Sai ya mika wa Gwamna Darius Ishaku cekin Naira miliyan 50 domin a bai wa wadanda rikici ya shafa.
Gwamna Ishaku ya gode wa dan kasuwar kan taimakon, ya ce gwamnati za ta tabbatar wadanda rikici ya shafa ne kawai aka raba wa kudin. Gwamnan ya shaida wa dan kasuwar cewa gwamnatin jihar da shi kansa ba su ji dadin yadda aka samu rigima a yankin Mambila ba.
Y a ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar kuma ya nemi al’ummar jihar su rungumi zaman lafiya don samun ci gaba mai dorewa.
Ita ma Hukumar NEMA ta kai taimakon kayan abinci da muhimman kayayyaki ga ’yan gudun hijirar a cikin manyan motoci 11.
Shugaban Hukumar Injiniya Mustpaha Maihaja ne ya gudanar da bikin soma raba tallafin a garin Gembu a makon jiya, inda ya ce raba kayan agajin bin umarnin Mukaddashin Shugaban kasa, Yemi Osibanjo na cewa a hanzarta kai agaji ga wadanda rikici ya shafa.
Ya ce Mukaddashin Shugaban kasa ya kuma ba da umarnin a gano bukatun ’yan gudun hijirar da inda aka tsugunar da su domin a ba su kular da ta kamata don rage musu kuncin da suke ciki.
Wakilin Sarkin Mambila, Dokta Bajo ya nuna godiyar al’ummar masarautar ga Mukaddashin Shugaban kasar sabo da damuwar da ya nuna ga halin da wadanda rikici ya shafa suke ciki.
Sarkin Fulanin Mambila, Alhaji Sa’idu Bawa ya gode wa Mukaddashin Shugaban kasar kan taimakon da ya bayar, kuma ya bayyana wa Babban Daraktan NEMA cewa sama da Fulani ’yan asalin yanki Mambila dubu 12 da 421 aka kona wa gidaje kuma yanzu haka suna gudun hijira a wurare daban-daban a Jihar Taraba da kasar Kamaru
Alhaji Bawa ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta taimaka wajen gina wa Fulani gidajensu da aka kone tare da ba su tallafin kudi don mayar da wasu daga cikin dukiyoyin da suka rasa.
Kayayyakin tallafin sun hada da buhunnan shinkafa da masara da gyero da sutura da kayan yara da katifu da tukwanen girki da man gyada da sabulan waka da na wanki.