Dangote ya ci gaba da rike kambin Attajirin Afirka

Shahararren dan kasuwar nan na Najeriya kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote  Alhaji Aliko Dangote ya sake zama wanda ya fi kowa dukiya a Afirka. Mujallar Forbes ta ce Dangote ya sake zama attajirin Afirka a bana wanda shi ne karo na tara  a jere. Mujallar Forbes ta wallafa sunayen wadanda suka fi kudi a Nahiyar […]

Dangote ya ci gaba da rike kambin Attajirin Afirka

Shahararren dan kasuwar nan na Najeriya kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote  Alhaji Aliko Dangote ya sake zama wanda ya fi kowa dukiya a Afirka. Mujallar Forbes ta ce Dangote ya sake zama attajirin Afirka a bana wanda shi ne karo na tara  a jere.

Mujallar Forbes ta wallafa sunayen wadanda suka fi kudi a Nahiyar Afirka ce a ranar Talatar da ta gabata, kuma attajiran sun fito ne daga kasashe 8 da ke Nahiyar Afirka da suka hada da: Masar da Afirka ta Kudu da kowace ke da manyan attajirai biyar sai kuma Najeriya wacce take da attajirai hudu sai Maroko wacce take da mutum biyu.

Alhaji Aliko Dangote mai shekara 62, ya sake kare kambunsa na attajirin Afirka ne da zunzurutun kudi Dala biliyan 10 da miliyan 100. Aliko Dangote ya shahara ne a harkar sana’anta siminti da harkokin fetur da iskar gas da fulawa da sukari. Kuma ya sha gaban dan kasar Masar Nassef Sawiri wanda yawan kudinsa ya kai Dala biliyan 8. Sawiri wanda yake da kamfannin gine-gine mai suna Orascom da kuma kamfanin takin zamani mafi girma a duniya da ke da rassa a biranen Tedas da Iowa na kasar Amurka.Haka yana da jari a kamfanonin siminti na Lafarge Holcim da Kamfanin Kayan Wasanni na Adidas.

Wanda ya zo na uku shi ne Mista Mike  Adenuga wanda kuma shi ne na biyu  a nan Nageriya, yana da dukiyar da ta kai Dala biliyan 7 da miliyan 700

Adenuga  wanda ya shahara a harkar banki da fetur, shi ne ya mallaki Kamfanin Sadarwa na Glo.

Wanda ke kankankan da Adenuga shi ne dan kasar Afirka ta Kudu, mai suna Oppenheimer da iyalansa wanda shi ma yake da dukiyar da ta kai Dala bilyan 7 da miliyan 700. Oppenheimer, ya mallaki kusan murabba’in mil 720 na gandun dajin da ke kasar Botswana da Zimbabwe da kuma Afrika ta Kudu ya shahara a harkar lu’u-lu’u a duniya.

Ga jerin sunayen Attajiran Afirka

1. Aliko Dangote, Dala biliyan 10.1

2. Nassef Sawiris, Dala biyan 8

3. Mike Adenuga, Dala biliyan 7.7

4. (3) Nicky Oppenheimer, Dala biliyan 7.7

5. Johann Rupert, Dala biliyan 6.5

6. Issad Rebrab, Dala biliyan 4.4

7. Mohamed Mansour,  Dala biliyan 3.3

8. Abdulsamad Rabi’u, Dala biliyan 3.1

9. Naguib Sawiris, Dala biliyan 3

10. Patrice Motsepe, Dala biliyan 2.6

11. Koos Bekker, Dala biliyan 2.5

12. Yasseen Mansour, Dala biliyan 2.3

13. Isabel dos Santos, Dala biliyan 2.2

14. Youssef Mansour, Dala biliyan 1.9

15. Aziz Akhannouch, Dala biliyan 1.7

16. Mohammed Dewji, Dala biliyan1.6

17. Othman Benjelloun, Dala biliyan 1.4

18. Michiel Le Roud, Dala biliyan1.3

19. Stribe Masiyiwa, Dala biliyan 1.1

20. Folorunsho Alakija, Dala biliyan 1