Dangote ya dawo matsayinsa na mai Arzikin Afirka
Alhaji Aliko Dangote, ya dawo kan matsayinsa na mutumin da ya fi kowa kudi a fadin Nahiyar Afirka
A rana guda Shugaban rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya dawo kan matsayinsa na mutumin da ya fi kowa kudi a fadin Nahiyar Afirka.
Dangote wanda dan asalin Jihar Kano ne ya karbe kambun ِBabban Attijirin Afirka, matsayin da ya dade a kai ne ’yan makonni bayan wani attajiri dan kasar Afirka a Kudu, Johann Rupert ya yi masa fintinkau.
Mujjalar Forbes da ke tattara alkaluma manyan masu kudin duniya, ta ruwaito cewa a ranar Litinin din nan Aliko Dangote ya ci wata gagarumar riba inda nan take ya doke Johann Rupert, ya dawo kan matsayinsa na mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka.
Rahotanni sun nuna ribar da attajirin ya samu ranar Litinin ta sa dukiyarsa karuwar da Dala biliyan 10 daga dala biliyan 9.5 da ke gareshi a a wancan makon.
Zuwa lokacin hada wannan labarin dukiyarsa ta kai Dala biliyan da ribar Dala miliyan 242, bisa ga alkalumam Forbes.
Forbes dai na bin diddigin dukiya da sauran abubuwan yau da kullun na manyan attajiran duniya inda gami da sabuntawa alkaluman a kai-akai domin gano matsayin kowane mutum da Forbes ta tabbatar a matsayin hamshakin attajiri.
Dangote yana da masana’anatar siminti, takin zamani da sukari, kuma shi ke da matatar mai mafi girma a Afirka, wato Matatar Mai ta Dangote, wadda wadda aka gina a kan sama da Dala biliyan 10.
Masan’atar simintinsa na samar da metrik ton miliyan 48.6 a duk shekara kuma yana da rassa a kasashen Afirka akalla 10.
Masana’antarsa ta takin zamani ta fara aiki a 2022 a Najeriya kuma a 2023 matatar mansa ta fara aiki.