Dangote ya fadi dalilin rashin bayar da irin tumatir

Hukumar Kamfanin Tumatir ta Dangote ta ce za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ba ta saba wa’adin da ta dauka na raba irin tumatir ga manoman tumatir a karkashin shirin nan na bayar da bashin noma na Babban Bankin Najeriya (CBN) ba, inda kamfanin ya ce tuni ya fara rarraba irin tumatir ga […]

Dangote ya fadi dalilin rashin bayar da irin tumatir

Alhaji Aliko Dangote

Hukumar Kamfanin Tumatir ta Dangote ta ce za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ba ta saba wa’adin da ta dauka na raba irin tumatir ga manoman tumatir a karkashin shirin nan na bayar da bashin noma na Babban Bankin Najeriya (CBN) ba, inda kamfanin ya ce tuni ya fara rarraba irin tumatir ga manoman.

Kamfanin ta bakin Manajan Daraktansa, Malam Abdulkarim Kaita lokacin da yake mayar da martani ga korafe-korafen da wadansu manoman tumatir ke yi cewa kamfanin ya hana su iri  kamar yadda aka yi alkawari a karkashin shirin bayar da bashin noma na CBN.

Manajan Daraktan ya ce tsaikon da aka samu ya faru ne dalilin wahalar da ake ciki na shigo da irin daga kasashen waje. “An fuskanci matsala ce wajen shigo da irin daga  waje, kodayake a yanzu kashi mafi yawa na irin ya riga ya sauka a nan Najeriya, kuma tuni aka fara rarraba irin ga manoman da aka riga aka tantance a karkashin shirin,” inji shi.

Tun farko Shugaban Kungiyar Manoman Tumatir ta Kasa reshen Jihar Kano, Alhaji Sani Yadakwari ya ce a yanzu haka fiye da manoma dubu 10 ne za su ci gajiyar bayar da bashin noman na Bankin CBN.

A cewarsa, Kamfanin Dangote zai rika karbar tumatir daga manoma dubu shida daga cikinsu.

Sai dai ya ce zuwa wa’adin da aka diba na raba irin wato ranar 15 ga Janairun nan,  kalilan  din manoman tumatir ne za su samu irin. “Mun sha zama da kamfanin inda muka yi yarjejeniyar cewa za a gama raba iri ga manomanmu a ranar 15 ga watan da muke ciki. Sai dai zuwa yanzu manoma kalilan ne suka samu irin. Ga shi wadansunsu sun zuba kudinsu masu yawa a harkar sai dai kuma daga dukan alamu ba za su samu tallafin a kan lokaci ba. Wannan abin takaici ne kwarai da gaske shi ya sa muke rokon kamfanin ya kara kokari wajen gudanar da aikin,” inji shugaban.