Dangote ya fara yunkurin saye kulob din Arsenal
Attajirin da ake ganin ya fi kowane kudi a Nahiyar Afirka a halin yanzu Alhaji Aliko dangote ya sake bayyana aniyarsa ta saye kulob din Arsenal da ke Ingila idan aka ba shi damar yin haka. Tun shekarar 2010 Alhaji Aliko dangote ya nuna sha’awar saye kulob din Arsenal amma masu kulob din suka ki […]

Attajirin da ake ganin ya fi kowane kudi a Nahiyar Afirka a halin yanzu Alhaji Aliko dangote ya sake bayyana aniyarsa ta saye kulob din Arsenal da ke Ingila idan aka ba shi damar yin haka.
Tun shekarar 2010 Alhaji Aliko dangote ya nuna sha’awar saye kulob din Arsenal amma masu kulob din suka ki amince masa da yin haka.
dangote dai yana daga cikin magoya bayan kulob din kuma an kiyasta yana da dukiyar da ta kai Dala biliyan 15 da digo 7 kwatakwacin Naira Tiriliyan 3 da miliyan 297.
A wata hira da ya yi da kafar sadarwar Boomber dangote ya ce : “Ina sa ran wata rana zan sayi kulob din Arsenal a farashin da ya dace. Zan yi tayin da masu kulob din ba za su iya kawar da kai daga gare shi ba, don tayi ne da zai ja ra’ayinsu don ganin sun sayar mini da shi”.
Dangote ya ce, duk da haka zai cigaba da karkata akalarsa wajen zuba jari a bangarori da dama don ya cigaba da bunkasa harkokin kasuwancinsa.
dangote dai ya zuba jari a bangarori da dama da suka hada da na sukari da kuma na fulawa. An ruwaito a kwanan nan ya zuba jarin da ya kai Dala biliyan 11 kwatankwacin Naira Tiriliyan 2 da biliyan 310 a matatar man da za ta rika samar da Gangar mai dubu 650 a kullum a wani gari da ke kusa da Legas. Haka kuma ya zuba jarida a kamfanin da ke samar da iskar gas da aka kiyasta ya kai Dala biliyan 2 da rabi kwatankwatin Naira biliyan 525.
Kulob din Arsenal dai an kiyasta zai kai farashin Fam miliyan 988 ko Dala biliyan 1 da miliyan 49 kwatankwacin Naira Biliyan 369 da miliyan 8.
A ranar 30 ga watan nan da muke ciki ne ake sa ran kulob din zai buga wasan karshe a gasar cin kofin kalubale na Ingila (FA) da kulob din Aston billa. Kulob din ne ya lashe kofin a bara.