Dangote ya hada hannu da Jamus don rage rashin aikin yi
Shugaban Gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce an zuba jarin Naira miliyan 345 a cikin shirin
Gidauniyar Dangote Foundation da hadin gwiwar wata kungiyar injiniyoyi ta kasar Jamus VDMA (German Association for Mechanical and Plant Engineering) da gidauniyarta ta Young Talent in Mechanical Engineering (NWS) sun kaddamar da wani shirin koyar da sana’o’i a Najeriya a wani kokari na cike gibi a fannin sana’o’i a dukkan sassan da suka shafi tattalin arzikin kasa.
A jawabinsa wajen kaddamar da shirin Shugaban Gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce an zuba jarin Yuro miliyan bakwai (kimanin Naira miliyan 345) a cikin shirin mai muhimmanci, kuma kaso mafitsoka zai tafi ne wajen bayar da horon kwarewa da samar da ingantattun kayan aiki da aka riga aka shigo da su daga kasar Jamus.
Ya ce za a sanya kayan ne a dakunan bayar da horo biyar da aka kakkafa domin wannan shiri a Kwalejin Bayar da Horo ta Dangote da ke Obajana.
Ya ce za a horar da wadanda za su ci gajiyar shirin da wadannan na’urori ta yadda za koya a aikace kuma su iya amfanar da sauran jama’a a lokacin da suka faragudanar da aiki.
Alhaji Aliko Dangote ya ce koyar da sana’o’in hannu da kanikanci suna da muhimmanci ga makomar tattalin arziki a matsayinsu na kashin bayan bunkasa ci gaba musamman a banagren sana’anta kayayyaki, inda Dangote ya ce, wannan shiri yana da burin magance babban gibin da ke akwai a bangaren sana’o’in hannu.
Ya ce,“Wadanda aka horar sun samu nasara samun horon da zai sa su zama kwararru a fannoni da dama, kuma sun samu cikakken horo mai inganci irin na ma’aikatanmu.”
Ministan Tattalin Arziki da Ci gaba na Jamus, Dokta Gerd muller, ya yaba wa Gidauniyar Dangote da Kungiyar VDMA kan samar da shirin da zai kawo sauyi tare da bunkasa tattlin arzikin Najeriya. Ya ce ma’aikatarsa ta tallafa wa shirin da Yuro miliyan3.6 kuma a shirye take ta kara tallafawa domin cimma nasarar shirin.
Tsohon Shugaban Kungiyar VDMA, Dokta Reinhold Fostge ya ce, ”Ina cike da farin cikin cewa wannan shiri ya tabbata a Najeriya. Mun faro ne a shekara shida da suka gabata.
Shekara hudu da suka gabata muka sanya hannu kan yarjejeniyar kafa shirin bayar da horo na Jamus da Najeriya. Shirin zai kara bunkasa kwarewar ma’aikata ya mayar da matasa wadanda za a iya dauka a aiki… manufarmu a VDMA ita ce nan gaba a rika musayar kwararrun ma’aikata a tsakanin Najeriya da Jamus, kuma a gaskiyar magana ba na da ja kan a gayyaci kwararru ’yan Najeriya su zo su taimake ni a Jamus ko na Jamus su zo Najeriya.”
A wani labarin Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya bukaci Gidauniyar Aliko Dangote da Kungiyar VDMA su tuna da Legas a kashi na biyu na horon da suke bayarwa tare da samar da kudin da za a fara wannan shiri abin yabo. Gwamnan ya ce, “Hakika na yi matukar farin cikin kasancewa wani bangare na wannan aiki na kawo canji a kasa… ga mu mutanen Legas ina murnar sanar da ku cewa muna da makarantun koyar da sana’o’i guda shida da muke kula da su sosai… kuma a yau ba kawai magana za mu yi a nan ba, muna sanar da jama’a
cewa bisa lura da abin da na ji a yanzu, ba za mu bar wannan ga Gidauniyar Dangote kawai ba, mu ma za mu kara ninka kokarinmu.
“Ba za mu jira ya yi wannan aiki a shiyyoyi shida na kasar nan ba. Jihar Legas za ta yi aiki da shi kuma tana so VDMA kan abin da take bukata daga gwamnatin jihar ta yadda nan ba da dadewa ba za mu gayyato daukacin makarantar Dangote zuwa Legas, ba za mu bari jan kafa irin na gwamnati ya kawo tsaiko ga wannan aiki ba, idan ta kama a tara kudi ne ake bukata ina ba ku tabbacin cewa Jihar Legas ta shirya wa haka. Kuma me ya sa muke wannan alkawari? Hakan saboda yadda muka ga Legas na da dimbin matasan da muke da su a kasarmu da jiharmu ne.
Legas ta ci gaba da kasancewa babbar mahadar tattalin arziki a kasarmu da kuma Afirka, kuma abin da ke gabanmu a yanzu shi ne damar da za mu hada gadar da za ta taimaka mana sosai wajen rage rashin aikin yi a jihar.” Da yake taya wadanda aka horar murna, Alhaji Dangote ya ce ya fahimci cewa sun zabo mutum 120 daga cikin 4000 da suka nemi hakan, inda ya ce hakan ya nuna su ne suka fi cancanta kuma suna da gaba mai kyau. Ya ce suna da yakini a kansu kuma suna fatar ganin abu mai kyau daga gare su, inda ya bukaci su yi amfani da damar da suka samu wajen zama masu amfani da amfanarwa ga kasar nan.
Ya yi alkawarin za a sake dibar wadansu matasan nan ba da jimawa ba, ta yadda dukkan sassan siyasa shida na kasar nan za su samu bunkasa ta hanyar shirin.