Dangote ya kara karya farashin dizel zuwa N940

Karo na uku ke nan da Dangote ke rage farashin man dizel; daga N1,700 zuwa N1,200 zuwa N1,000 sannan zuwa N940

Dangote ya kara karya farashin dizel zuwa N940

Matatar Man Dangote ta kara karya farashin litar man dizel zuwa N940, man jirgin sama kuma N980.

Ragin farashin na zuwa ne kimanin mako biyu da kamfanin ta rage farashin litar man dizel zuwa N1,000 daga N1,200.

Kamfanin ya sanar da cewa masu sayen lita miliya zuwa sama a matatar ne za su samu a kan N940, amma masu lita 5,000 zuwa sama kuma a kan N970.

Kakakin rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya ce saukin da aka samu na daga cikin yunkurin kamfanin na ganin an samu saukin rayuwa da na kayayyaki a Najeriya.

“Matatar Man Dangote ta kulla yarjejeniya da Kamfanin Man MRS don ganin jama’a suna samun mai a farashi mai sauki a gidajen man MRS a fadin Najeriya.”

Ya kara da cewa za a fadada yarjejeniyar zuwa wasu manyan kamfanonin mai da ke sha’awa.

Karo na uku ke nan da Dangote ke rage farashin man dizel; daga N1,700 zuwa N1,200 zuwa N1,000 sannan zuwa N940, wanda Shugaba Bola Tinubu ya jinjina wa kamfanin.

Shugaban kungiyar masu masana’antu ta Najeriya (MAN), Ajayi Kadiri, ya yaba wa kamfanin Dangote yana mai cewa hakan na nuna kamfanonin cikin gida za su iya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

“Ragin farashin zai kawo saukin a bangaren masana’antu, sufuri da noma da dai sauransu wanda hakan zai yi tasiri wajen kawo raguwar farashin kayyyaki a kas,” inji shi.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja