Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas
Matatar ta ce ta rage farashin ne saboda albarkacin watan azumin Ramadan.

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 860 kan kowace lita a Jihar Legas.
Yanzu haka dai an samu ragin Naira 65, daga farashin da ake siyarwa a baya.
- Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje
- Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno
Sabon farashin zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.
Matatar ta ce wannan matakin na nufin rage wa ‘yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta, yayin da azumin watan Ramadan ke ƙaratowa, tare da tallafa wa manufofin tattalin arziƙi na Shugaba Bola Tinubu.
“Rage farashin man fetur wani ɓangare ne na ƙokarinmu na sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya,” in ji matatar Dangote.
“Za mu ci gaba da tabbatar da wadatar man fetur a farashi mai sauƙi.”
Wannan ragi, na nufin za a sayar da man fetur a gidajen mai a Legas kan Naira 860 kan kowace lita, Naira 870 a Kudu maso Yamma, da Naira 880 a Arewacin Najeriya.
A gidajen mai na AP da Heyden, farashin zai kasance Naira 865 a Legas, sai Naira 875 a Kudu maso Yamma, da Naira 885 a Arewacin Najeriya.
“Muna kira ga ‘yan kasuwa su mara mana baya don tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ci gajiyar wannan sauƙi,” in ji matatar.