Dangote ya rufe kamfanin simintinsa na Tanzaniya
Shugabanin Rukunin Kamfanin dangote Alhaji Aliko dangote ya rufe kamfanin simintinsa da ke kasar Tanzaniya saboda tashin farashin makamashi, kamar yadda wasu jami’an gwamnatin kasar suka bayyana. Shugabannin reshen kamfanin a Tanzaniya sun yi korafin cewa gazawar gwamnati na samar musu da makamashi mai sauki da kuma sauran matsalolin gudanarwa.Kamfanin ya taba gabatar da bukatarsa […]

Shugabanin Rukunin Kamfanin dangote Alhaji Aliko dangote ya rufe kamfanin simintinsa da ke kasar Tanzaniya saboda tashin farashin makamashi, kamar yadda wasu jami’an gwamnatin kasar suka bayyana.
Shugabannin reshen kamfanin a Tanzaniya sun yi korafin cewa gazawar gwamnati na samar musu da makamashi mai sauki da kuma sauran matsalolin gudanarwa.
Kamfanin ya taba gabatar da bukatarsa ga kamfanin makamashin kasar, wato Tanzania Petroleum Debelopment Corporation (TPDC), inda yake so a rika ba shi iskar gas a kan farashi mai rahusa, bukatar da gwamnatin ta ki amincewa da shi, kamar yadda kafar yada labarai ta Forbes ta bayyana.
Kamfanin dangote ya kashe kimanin Dala miliyan hudu a kan man dizil a kowane wata wajen tafiyar da kamfanin simintin.
“Kamfaninmu yana amfani da lita miliyan shida na man dizil wajen tafiyar da injin janareta, bayan an kasa cika alkawarin da aka yi mana na ba mu isakar gas,” inji Jami’in Gudanarwar Kamfanin a Tanzaniya Harpeet Duggal.
An gina kamfanin ne a garin Mtwara wadda yake yakin Kudu-maso-Gabashin kasar, saboda a samu iska mai rahusa don ana hakota a kusa da garin. Tsohuwar Gwmnatin Shugaba Jakaya Kikwete ta yi wa kamfanin alkawarin samar mata da iskar gas, kamfanin TPDC ya ki cika alkawarin a karkashin Shugaban kasa John Magufuli. A wani kokari na rage kudin makamashin da suke amfani da shi, Kamfanin simintin ya fara shigo da kwal daga kasar Afirka ta Kudu mai makwabtaka, wanda yake da arha fiye da iskar gas. Wannan ya fusata manyan jami’an gwamnatin Magufuli musamman saboda ganin yadda gwamnatin Tanzaniya ita ma tana da dimbin arzikin kwal.
A watan Agusta, gwamnatin ta hana shigo da kwal daga Afirka ta Kudu, wani abu da masu sharhi suke ganin an dauki matakin ne don kamfanin simintin.
Gwamnatin Tanzaniya ta sha yin kira ga kamfanin da cewa ya rika sayen kwal din kasar, sai dai manyan jami’an kamfanin sun sha yin korafi a kan cewa wurin da ake hako kwal din ya yi nisa daga kamfanin kuma ba shi da inganci, har ila yau, yana da tsada.
Kodayake, Mukaddashin Kwamishinan Ma’adanan a Ma’aikatar makamashi da Ma’adanai John Shija, ya ce kwal din kasar ya fi wanda ake shigowa da shi daga kasashen waje kyau da sauki.
“Yayin da kwal din Tanzaniya ana sayar da tan daya a kan Dala 90, idan aka hada da kudin sufurinsa. Amma ana samun na Afirka ta Kudu a tsakanin Dala 103 zuwa 118 kowane tan daya, duk da kudin sufurinsa,” inji Shija.