dangote ya shawarci ’yan Najeriya kan tattalin arziki

Shugaban Kamfanin dangote, Alhaji Aliko dangote ya bukaci ’yan Najeriya su rika kallon kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin kasar a matsayin wata alama da za ta zaburar da su har su yi aiki tukuru wajen gina kasarsu. Hamshakin dan kasuwar ya yi furucin ne yayin da ’yan kungiyar dillalan siminti ta kasa suka kai […]

dangote ya shawarci ’yan Najeriya kan tattalin arziki
dangote ya shawarci ’yan Najeriya kan tattalin arziki

Shugaban Kamfanin dangote, Alhaji Aliko dangote ya bukaci ’yan Najeriya su rika kallon kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin kasar a matsayin wata alama da za ta zaburar da su har su yi aiki tukuru wajen gina kasarsu.

Hamshakin dan kasuwar ya yi furucin ne yayin da ’yan kungiyar dillalan siminti ta kasa suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Jihar Legas a makon jiya.
Ya ce matsalar tattalin arziki ta shafi kasashe da dama a duniya ciki har da Najeriya, sannan ya tabbatar da za a iya shawo kan lamarin idan aka dauki matakan da suka dace.
Ya kara da cewa kamata ya yi lamarin ya zama wani mataki da kasar za ta zama mai karfin tattalin arziki nan gaba.
Ya bayyana cewa har yanzu Najeriya kasa ce da masu sanya hannayen jari suke sha’awa duk da kalubalen tattalin arzinki da na tsaro da kasar take fuskanta.
Ya ce idan aka ba gwamnati goyon baya duk kalubalen da ke fuskantar Najeriya za su zama tarihi, kuma kasar za ta zama mai karfin tattalin arziki.
“Na sha fada cewa Najeriya kasa ce da ’yan kasuwa suke sha’awar zuba hannayen jarinsu. Allah Ya ba mu abubuwa masu yawa da Bai ba wadansu kasashe ba. Muna da albarkar kasar noma, muna da ma’adanai muna da mai. Abin da muke bukata shi ne mu yi amfani da wadannan abubuwa ta hanya mai kyau.
“Kada mu bari kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu ya sanyaya mana gwiwa wajen bunkasa tattalin arzikinmu. Kada su hana mu sanya hannayen jari. Mu dauka halin da muke ciki ya wuce. kasashe da dama sun fuskanci irin wannan kalubale a baya, ina so mu dauki wannan lamari a matsayin wani matakin da zai karafafa mana gwiwa mu cimma burinmu.” Inji shi.