Dangote ya zama attajiri na 25 a duniya

A yanzu haka hamshakin dan kasuwan nan kuma shugaban rukunin kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dagote ya zama na 25 a jerin masu kudin duniya saboda mallakar dala biliyan 20 da ya yi.Mujallar Forbes da ake bugawa a kasar Amurka wacce take buga labaran masu arziki da fitattun mutane a duniya ita ce ta bayyana haka […]

Dangote ya zama attajiri na 25 a duniya
Dangote ya zama attajiri na 25 a duniya

A yanzu haka hamshakin dan kasuwan nan kuma shugaban rukunin kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dagote ya zama na 25 a jerin masu kudin duniya saboda mallakar dala biliyan 20 da ya yi.
Mujallar Forbes da ake bugawa a kasar Amurka wacce take buga labaran masu arziki da fitattun mutane a duniya ita ce ta bayyana haka a karshen makon da ya gabata, inda ta ce dangote har yanzu shi ne wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka baki daya.
Mujallar ta bayyana cewa kudin da ya samu sakamakon tashin farashin hannayen jarin kamfanin simintinsa mai suna dagote Cement Plc  a kasuwar hada-hadar hannun jari ta Najeriya inda aka sayar da kowane hannun jari daya a kan naira 191 a ranar juma’ar da ta gabata shi ya ba shi damar mallakar tsabar kudi har Dala biliyan 20.
Ta kara da cewa, hakan ya sanya ya kasance dan Afirka na farko da ya mallaki dala biliyan 20  wanda hakan ya sanya zai cimma burinsa na kasancewa daya daga cikin mutane biyar da suka fi kowa kudi a duniya baki daya.
Ta ci gaba da cewa, tashin hannun jarin kamfanin siminti na dangote ya sanya kamfanin ya kasance kamfani na farko a Najeriya da ya mallaki jarin Dala biliyan 20.
Mujallar ta bayyana cewa hannayen jarin da ya mallaka na kashi 93 a bangaren siminti kawai a yanzu ya kai Dala biliyan 19 da rabi.
Saboda haka mujallar ta kara da cewa, idan aka yi la’akari da hannayen jarin da ya mallaka a kamfanoni masu zaman kansu kamar kamfanin siga na dangote da kamfanin gishiri da bankin Zenith da bankin UBA da kamfanin filawa da harkar gine-gine da kamfanonin jiragen sama da na ruwa da makuden kudin da ya samu kwanan nan daga ribar da aka samu daga kamfanin siminti na Dala miliyan 300 za a iya cewa dangote ya mallaki abin da ya fi Dala biliyan 20.
Dadin-dadawa, mujallar ta bayyana cewa a yanzu dangote ya fi mai arzikin nan dan kasar Rasha mai suna Alisher Usmanob  da mai kudin nan dan kasar Indiya mai suna Lakshmi Mittal kudi.
Haka zalika mujallar ta ce, a yanzu haka dangote na yin kunnen doki da mai arzikin nan na kasar Indiya mai suna Mukesh Ambani kuma ma ana tsammanin zai iya wuce shi idan aka yi la’akari da yadda dukiyarsa ke saurin bunkasa da karuwa.
Sakamakon haka mujallar ta bayyana cewa, a yanzu dangote na neman kamo hamshakin makudin nan mai kamfanin sadarwa na Google dan kasar Amurka mai suna Larry Page da kuma hamshakin mai kudinnan mai suna Sergey Brin.