dangote zai ciyar da duk ’yan gudun hijirar Boko Haram a azumin bana

Attajirin Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote ya yi alkawarin ciyar da daukacin ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a cikin watan azumin Ramadan din bana.Alhaji Aliko dangote ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin day a ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira na […]

dangote zai ciyar da duk ’yan gudun hijirar Boko Haram a azumin bana
dangote zai ciyar da duk ’yan gudun hijirar Boko Haram a azumin bana

Attajirin Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote ya yi alkawarin ciyar da daukacin ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a cikin watan azumin Ramadan din bana.
Alhaji Aliko dangote ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin day a ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira na Dalori da Bakassi da ke garin Maiduguri fadar Jihar Borno, inda kuma ya yi alkawarin bayar da tallafin Naira biliyan domin kula da ’yan gudun hijirar na Boko Haram.
Akwai akalla ’yan gudun hijirar da yaki da Boko Haram ya raba da muhallinsu fiye da miliyan biyu da dubu 200 da suka fito daga yankin Arewa maso Gabas.
dangote ya yi alkawarin magance yunwa a sansanonin ’yan gudun hijirar da suke Jihar Borno, inda ya ce zai rika kai abincin da ake bukata ga mutanen da aka raba da muhallinsu a cikin watan azumin Ramadan mai zuwa.
dan kasuwar ya ce Gidauniyar dangote ta riga ta kashe kimanin Naira biliyan daya da miliyan 400 a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, amma a cewarsa wannan bai wadatar ba, kuma shi ne “Dalilin da ya sa na zo nan domin in gane wa idona; ina ba ku tabbacin za mu ci gaba da hada hannu da gwamnatocin jihohin da na tarayya domin kawar da yunwa daga sansanonin,” inji dangote.
Ya ce gidauniyarsa za ta kebe Naira biliyan biyu don kula da sansanonin ’yan gudun hijirar domin bai wa gwamnatin Jihar Borno damar mayar da hankali wajen gudanar da wasu ayyukan raya kasa.
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima wanda ya zubar da hawaye kan tallafin na dangote, ya yi ta addu’o’in alheri ga dan kasuwar.
“Yau ba rana ce ta dogon surutu ba, don haka ina rokon Allah Madaukaki Ya ci gaba da sanya maka albarka, kuma mun gode,” Gwamna yake shaida wa dangote.
dangote, wanda ya kai ziyarar girmamawa ga Mai martaba Shehun Borno Alhaji Umar Garbai Ibn El-Kanem, ya kuma alkawarin zai sanya hannu wajen zuba jari a Jihar Borno duk lokacin da kurar Boko Haram ta kwanta.
Ya ce, “Kamar yadda na fadi da farko wannan ziyara tamu ba za ta kasance ta karshe ba, za mu ci gaba da hada hannu da gwamnatin Jihar Borno domin samar da aiki ga jama’armu, kuma ina tabbatar maka duk abincin da za a bukata a lokacin azumin watan Ramadan a sansanonin ’yan gudun hijirar, Gidauniyar dangote za ta samar da shi domin saukake wahalar da mutanenmu suke ciki.”
Shehun ya gode wa dangote kan alkawuran da ya yi, inda ya ce tallafin Naira biliyan biyu da ya bayar shi ne tallafi mafi girma da wani mutum ya bayar don kula da ’yan gudun hijirar.
 “Yanzu da ka bayar da Naira biliyan biyu ga ’yan gudun hijirar, wannan tallafi zai sanya ’yan gudun hijirar cikin farin ciki, saboda wannan ne tallafi mafi girma a saninsa, kuma za a dade ana tunawa da shi,” inji Shehun Bornon.