dangote zai dauki ma’aikata dubu 150 aiki
A kokarin da suke yi wajen samar da ayyukan yi rukunonin kamfanin dangote za su samar da guraben ayyukan yi ga mutum dubu 150 a bangorin kamfanin daban-daban. Furucin ya fito ne daga bakin babban daraktan masu ruwa da tsaki da kuma yada labarai na kamfanin, Injiniya Ahmed Mansur a wajen bikin baje kolin kasuwar […]
A kokarin da suke yi wajen samar da ayyukan yi rukunonin kamfanin dangote za su samar da guraben ayyukan yi ga mutum dubu 150 a bangorin kamfanin daban-daban.
Furucin ya fito ne daga bakin babban daraktan masu ruwa da tsaki da kuma yada labarai na kamfanin, Injiniya Ahmed Mansur a wajen bikin baje kolin kasuwar duniya da ake gudanarwa a Legas, inda ya ce kamfanin zai samar da ayyukan ne don bayar da gudunmawarsa wajen bunkasa tattalin arziki.
Ya ce baje kolin da ake yi a jihar Legas ya zama wata kafa inda kamfanoni za su baje kayan da suke sayarwa don samun abokanen hulda masu yawa.
Mansur ya ce kamfanin zai fadada ayyukansa daga harkar suminti da sukari zuwa man fetur da iskar gas don bunkasar tattalin arzikin kasa.
Saboda haka ya ci gaba da cewa a yanzu haka kamfanin yana gina katafariyar masana’artar tace man fetur, wacce za ta kawo karshen shigo da mai da kuma masana’artar takin zamani, wacce za ta inganta harkar samar da abinci a kasa baki daya.
Hakazalika, ya bayyana cewa kamfanin ya fadada harkarsa ta samar da shinkafa inda ya sanya makuden kudi don bunkasa harkar.
Daga nan sai ya ce ya sanya makuden kudi a harkar samar da ingantaccen sukari don bunkasar suga a kasa baki daya.