Dangote zai kashe Dala miliyan 100 kan yaki da yunwa a Najeriya
Cibiyar Aliko Dangote ta yi alkawarin kashe Dala miliyan 100 a cikin shekara biyar don tumkarar tamowa a wasu sassan kasar Najeriya. Dangote ya yi alkawarin a taron da aka kammala kan Matsalar Tawowa na shekarar 2017 wanda aka gudanar a garin Milan na kasar Italiya wanda jami’an gwamnati da kungiyoyin kasa da kasa da […]

Cibiyar Aliko Dangote ta yi alkawarin kashe Dala miliyan 100 a cikin shekara biyar don tumkarar tamowa a wasu sassan kasar Najeriya.
Dangote ya yi alkawarin a taron da aka kammala kan Matsalar Tawowa na shekarar 2017 wanda aka gudanar a garin Milan na kasar Italiya wanda jami’an gwamnati da kungiyoyin kasa da kasa da ’yan kasuwa suka halarta.
Shugaban cibiyar Dangote, Zouera Youssoufou ya ce yawan tamowa a Najeriya na kawo cikas ga bunkasar lafiyar yara da rayuwarsu da bunkasar tattalin arziki.