dangote zai kashe fiye da Tiriliyan daya wajen gina matatar mai a Legas

Hamshakin dan kasuwan nan Alhaji Aliko dangote zai kashe naira tiriliyan daya da dubu dari biyar wajen kafa kamfanin matatar mai  a unguwar Lekki da ke jihar Legas.Gwamnan jihar Legas Babatunde Raji Fashola shi ne ya kaddamar da shirin tare da gabatar da dangote ga al’ummar yankin.Kamar yadda dangote ya ce,  yankin Lekki zai kasance […]

dangote zai kashe fiye da Tiriliyan daya wajen gina matatar mai a Legas

Hamshakin dan kasuwan nan Alhaji Aliko dangote zai kashe naira tiriliyan daya da dubu dari biyar wajen kafa kamfanin matatar mai  a unguwar Lekki da ke jihar Legas.
Gwamnan jihar Legas Babatunde Raji Fashola shi ne ya kaddamar da shirin tare da gabatar da dangote ga al’ummar yankin.
Kamar yadda dangote ya ce,  yankin Lekki zai kasance shiyyar kasuwanci mafi girma a nahiyar Afirka baki daya.
Ya ce, ‘idan muka duba abin da gwamnati ta yi na kawo kasuwanci wannan wuri ina mai tabbatar muku da cewa wannan wuri zai kasance wurin kasuwanci mafi girma a nahiyar Afirka. Na san mutane za su fara nuna gamsuwa da abin da ya faru.’
Alhaji Aliko dangote wanda shi ne attijirin da ya fi arziki a nahiyar Afirka kuma na 30 a jerin masu kudin duniya, ya bayyana cewa matatar man za ta samar da dubban ayyukan yi ga masu neman aiki.
Ya bayyana  cewa, yankin Lekki zai samar da alfanu ga jihar Legas  da kasa baki daya, ‘Misali babu yadda za a ce mun sanya kudinmu  har naira biliyan tara a nan ba tare da tabbatar da cewa yankin zai bunkasa ba. Saboda haka za mu yi aiki tukuru cikin gaggawa don cim ma burin da ake so,’ In ji shi
Ya ci gaba da cewa, ‘ al’ummar yankin za su amfana da shirin don mutum dubu takwas za su sami horo tare da samar da ayyuka ga matasan yankin.’’
Sarakunan yankin da shugabannin  matasan yankin sun nuna farin cikinsu dangane da shirin, inda suka yi fatan shirin zai bunkasa yankin.
Shi kuwa gwamna Fashola cewa ya yi, ‘mun cim ma yarjejeniya a gaban jama’a. Mun yi magana da yaren jama’ar yankin, wannan ya nuna cewa jama’ar yankin  sun ba da goyon baya kuma sun nuna suna son a kafa kamfanin a yankinsu.