Dangote zai tallafa wa wasanni a Jihar Nasarawa

Kamfanin Sukari na Dangote ya kudiri aniyar tallafa wa ci gaban wasanni a Jihar Nasarawa. Janar Manajan Kamfanin, Mista Beberly Martin ne ya fadi haka a garin Tunga da ke Karamar Hukumar Awe yayin da Kwamishinan Wasanni, Alhaji Othman Bala-Adams ya kai masa ziyara. Ya ce Kamfanin Dangote zai tallafa wa ci gaban wasanni inda […]

Dangote zai tallafa wa wasanni a Jihar Nasarawa

Kamfanin Sukari na Dangote ya kudiri aniyar tallafa wa ci gaban wasanni a Jihar Nasarawa.

Janar Manajan Kamfanin, Mista Beberly Martin ne ya fadi haka a garin Tunga da ke Karamar Hukumar Awe yayin da Kwamishinan Wasanni, Alhaji Othman Bala-Adams ya kai masa ziyara.

Ya ce Kamfanin Dangote zai tallafa wa ci gaban wasanni inda ya ce har an yi tsari gamsasshe da zai tallafa wa matasa da yawa.

Mista Martin ya kara da cewa, “Akwai kudin da kamfanin ya kebe domin ci gaban jama’ar garin da kamfani yake don a tallafa musu, amma muna bukatar a rubuta tsari a bayyane domin ci gaban kowa kuma a tabbatar da ci gaban tsarin na lokaci mai tsawo.”

A jawabi Kwamishinan ya ce, sun yi murna da tarbar da aka yi musu, sannan ba za su bada kunya ba.