dangwari mai karya
Wani dangwari ne da ma al’adarsu ce idan an haifi yaro sai a rika koya masa karya. To akwai wani rafi kusa da inda ake zuwa koya wa yaro karyar. Sun kama hanya zuwa ke nan, sun zo tsallaka rafin sai baban ya buga ihu ya ce: “Kai, kai yaro, na taka kifi.” Sai yaron […]
Wani dangwari ne da ma al’adarsu ce idan an haifi yaro sai a rika koya masa karya. To akwai wani rafi kusa da inda ake zuwa koya wa yaro karyar. Sun kama hanya zuwa ke nan, sun zo tsallaka rafin sai baban ya buga ihu ya ce: “Kai, kai yaro, na taka kifi.” Sai yaron ya kada baki ya ce: “Lallai shi ya sa na ji maikon kifin a bakina.” Sai baban ya ce: “Ah, ah, lallai yaro ka yi nisa, bari mu koma gida.”
Daga Iliyas Idris Fahad Suleja