Dani Albes ya sabunta kwantaraginsa a FC Barcelona

dan kwallon baya a kulob din FC Barcelona da ke Sifen, Dani Albes ya kawo karshen rade-radin da ake bazawa na cewa zai bar kulobh din a karshen kakar wasa ta bana, bayan ya sabunta kwantaraginsa a ranar Talatar da ta wuce. Albes ya sabunta kwantaraginsa na tsawon shekara biyu ne a kulob din. Yanzu […]

Dani Albes ya sabunta kwantaraginsa a FC Barcelona
Dani Albes ya sabunta kwantaraginsa a FC Barcelona

dan kwallon baya a kulob din FC Barcelona da ke Sifen, Dani Albes ya kawo karshen rade-radin da ake bazawa na cewa zai bar kulobh din a karshen kakar wasa ta bana, bayan ya sabunta kwantaraginsa a ranar Talatar da ta wuce.

Albes ya sabunta kwantaraginsa na tsawon shekara biyu ne a kulob din. Yanzu kwantaragin zai kare ne a shekarar 2017 maimakon ranar 30 ga wannan wata da muke ciki.
dan shekara 32, haifaffen Brazil, Albes a da kwantarabinsa za ta kare da kulob din ne daga ranar 30 ga wammam wata na Yuni da muke ciki amma sai suka sasanta da kulob din al’amarin da ya sa aka tsawaita kwantaragin nasa da shekara biyu. Sannan yarjejeniyar ta nuna za a iya kara masa shekara daya idan ya cigaba da tabuka abin kirki kafin wa’adin kwantaragin ya kare.
Tun cikin shekarar 2008 Dani Albes ya koma Barcelona daga Sebilla inda kawo yanzu ya buga wa kulob din wasanni 343 da hakan ta sa ya kasance na farko a ’yan kwallon kulob din wadanda ba ’yan asalin Sifen ba da ya fi buga wa kulob din yawan wasanni.
Kawo yanzu dan kwallon ya samu nasarar lashe kofuna 19 a kulob din da suka hada da kofunan La-Liga sau biyar da kofunan zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) sau uku da kofunan kalubale na Sifen (Spanish Cup) sau uku da kofunan European Super Cups sau biyu da kofunan Spanish Super Cup sai hudu da kuma kofunan Club World Cup sau biyu.
Yana daga cikin ’yan kwallon Barcelona bakwai da suka kafa tarihin lashe kofuna uku a kmakar wasa daya watau a shekarar 2008 zuwa 2009 da kuma a bana.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram