Daniel Amokachi ya zama kocin Ifeanyi Ubah

Tsohon mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Superr Eagles Daniel Amokachi ya zama sabon kocin kulob din Ifeanyi Ubah da ke Anambra. A ranar Lahadin da ta wuce ne dai kulob din ya gabatar da Amokachi ga magoya bayan kulob din a matsayin sabon koci a filin wasansu mai suna Rojenny International Stadium da ke […]

Daniel Amokachi ya zama kocin Ifeanyi Ubah
Daniel Amokachi ya zama kocin Ifeanyi Ubah

Tsohon mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Superr Eagles Daniel Amokachi ya zama sabon kocin kulob din Ifeanyi Ubah da ke Anambra.

A ranar Lahadin da ta wuce ne dai kulob din ya gabatar da Amokachi ga magoya bayan kulob din a matsayin sabon koci a filin wasansu mai suna Rojenny International Stadium da ke Oba na Jihar Anambra.
An gabatar da kocin ne a lokacin da kulob din zai kara da na Sunshine Stars a gasar rukunin firimiya na Najeriya sai dai saboda ruwan sama da ya yi tsanani inda ya mamaye filin wasan ta sa aka daga wasan sai washegari. Sai dai a wasan da ya gudana a washegari an tashi ne babu ci watau 0-0 a tsakanin Ifeanyi Ubah da na Sunshine Stars da ke Akure. Kawo yanzu kulob din Ifeanyi Ubah yana matsayi na 13 ne daga jerin kungiyoyi 20 da ke fafatawa a gasar rukunin firimiya na Najeriya da aka fi sani da GLO Premier League.
Amokachi, wanda ya taba zama kocin Nasarawa United ya zama sabon kocin Ifeanyi Ubah ne bayan kulob din ya daga darajar tsohon kocinsu John Obu zuwa Mai ba kocin shawara (Technical Director).
Daniel Amokachi, dan kimanin shekara 42 ana masa lakabi ne da “Bull” a lokacin da yake kwallo an dauke su a kulob din Ifeanyi Ubah ne tare da tsohon golan Super Eagles Ike Shoronmu. Ike Shoronmu an dauke shi ne a matsayin mai horar da gololin da ke kulob din na Ifeanyi Ubah.
A wata tattaunawa da aka yi da shi Daniel Amokachi ya nuna farin cikinsa a kan wannan matsayi da kulob din ya ba shi na horar da ’yan kwallon. Ya ce ko shakka babu zai yi kokari wajen ganin ya ba marada kunya.