danjuma ga Jonathan: Ka jagorance mu zuwa dajin Sambisa
Tsohon Ministan Tsaro Laftanar-Janar Theophilos danjuma ya shaida wa Shugaba Goodluck Jonathan cewa ’yan Boko Haram su ne ke samun galaba a halin yanzu.Janar din mai ritaya, ya fadi haka ne a Fadar Shugaban kasa, yayin kaddamar da Gidauniyar Tallafa wa Wadanda ’Yan Boko Haram suka jigata, a shekaranjiya Laraba. Ya kara da cewa yaki […]

Tsohon Ministan Tsaro Laftanar-Janar Theophilos danjuma ya shaida wa Shugaba Goodluck Jonathan cewa ’yan Boko Haram su ne ke samun galaba a halin yanzu.
Janar din mai ritaya, ya fadi haka ne a Fadar Shugaban kasa, yayin kaddamar da Gidauniyar Tallafa wa Wadanda ’Yan Boko Haram suka jigata, a shekaranjiya Laraba. Ya kara da cewa yaki da tu’annatin ’yan Boko Haram ya dauki dogon lokaci kuma ya zama wajibi a kawo karshen ta’addancin nasu nan da ba dadewa ba.
Ya bayyana cewa wasu mutane na ganin rikicin Boko Haram a matsayin aikin ta’addanci, shi kuwa ya ce tun lokacin da al’amarin ya fara, ya bayyana shi da yakin basasa.
Kamar yadda ya ce, ’yan Boko Haram suna zaben wuraren da suke kai wa hari amma kuma suna samun galaba, a yayin da suke daidaita al’ummar Najeriya.
“Ya zama wajibi a kawo karshen wannan yaki. Dole ne mu ci galabar yakin nan da dan lokaci kankane, domin kuwa a halin yanzu ya dauki dogon lokaci. Na kira shi da sunan yakin basasa a lokacin da ya fara, a lokacin da mutane ke kiransa da ta’addanci. Wannan ya nuna cewa ’yan Boko Haram suke kan gaba da nasara a halin da ake ciki, sukan zabi wuraren duk da suke son kai hari. Ta kai ga ma har sukan yi tunga a wuraren da suka ci galabarsu. Ya zama tilas mu yi nasarar wannan yaki,” inji shi.
Game da bukatar da Jonathan ya yi musu cewa su shiga ko’ina kuwa, saidanjuma ya ce sai idan Shugaba Jonathan a matsayinsa na babban kwamanda ya shiga gaba ya jagorance su sannan za su je dajin Sambisa, inda nan ne ’yan Boko Haram suka yi tunga.
“Ya Shugaba, abu daya da ba za mu yi ba shi ne shiga Dajin Sambisa. Babban Kwamadan Sojan Najeriya (Shugaba Jonathan), shi zai jagorance mu, sannnan mu bi bayansa. Za mu tattara kudi, za mu rarraba tallafi. Na yi maka alkawari, za mu yi aikinmu cikin jajircewa da gaskiya, amma lallai sai mun yi nasarar wannan yaki. Allah Ya yi wa kasar nan albarka,” inji danjuma, a yayin da yake dariyar raha.