‘Dankalin Hausa ya zama abincin ’yan Kudu’

Dankali ya kasu kashi biyu: akwai na Hausa da na Turawa.

‘Dankalin Hausa ya zama abincin ’yan Kudu’

Dankalin Hausa

Dankali wani abinci ne da aka fi nomansa a Arewacin Najeriya da wasu yankunan Kudu.

Dankali ya kasu kashi biyu: akwai na Hausa da na Turawa.

A tattaunawar Aminiya da wani mai sayar da Dankalin Hausa mai suna Ahmad Sheka a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, ya ce dankali tamkar kayan gwari ne, tunda idan mutum ya kawo akalla buhu 20 kafin ya kare sai sama da buhu 7 sun lalace.

Wannan shi ne kalubalen da sayar da dankali.

Ya ce, “Dankali da farko iri biyu ne, wato Dankalin Hausa da kuma wanda ake kira da na Turawa.

“Mafi yawan Dankalin Hausa a Arewacin Najeriya ake nomansa. A iyakar sanina wuraren da ake noman dankalin sun hada da yankin Zariya da abin da ya gangara Kano da Jigawa”.

Ya ce abubuwan da ake yi da dankalin suna da yawa.

Ana iya cin sa tun yana danye ko a gasa ko kuma a dafa shi. Idan kuma an kai gida ana iya soya shi saboda haka abu ne mai amfani.

Ya ce dankali yana daya daga cikin cimakar mutanen Arewa da a yau ’yan Kudu suke neman su kwace domin su ma suna ci, suna nomawa, domin kuwa ga shi nan ana kawo shi mota-mota, kuma su suke saye akasarinsa, duk cewa da cewa mutanen Arewa ne suke kawo shi.