dankwalisa ya fitar da albam din ‘Nafarko’
Wani fitaccen mawaki mai suna Ibrahim Aya Abdullahi da ke Jihar Legas ya fitar da sabon faifan wakokinsa mai suna ‘Nafarko’. Ibrahim wanda ake yi masa lakabi da dankwalisa ya bayyana wa Aminiya cewa faifan wakokin ya kunshi wakoki biyar.Ya ce “Na sanya wa sabon albam din wakokina ‘Nafarko’ saboda shi ne albam din da […]
Wani fitaccen mawaki mai suna Ibrahim Aya Abdullahi da ke Jihar Legas ya fitar da sabon faifan wakokinsa mai suna ‘Nafarko’.
Ibrahim wanda ake yi masa lakabi da dankwalisa ya bayyana wa Aminiya cewa faifan wakokin ya kunshi wakoki biyar.
Ya ce “Na sanya wa sabon albam din wakokina ‘Nafarko’ saboda shi ne albam din da na fara fitarwa a rayuwata, na yi wakokin ne don in ilimantar da jama’a, kuma in nishadantar da su tare da nusar da su wasu batutuwan rayuwa. Akwai wakoki biyar a cikin albam din kamar wakar da na sa mata suna ‘’Yan Agege’ da wakar ‘Sarkin Samarin Agege’ da wakar ‘Masoya’ da wakar ‘KB Yerima’ da kuma waka mai suna ‘Duniya’.
Ya ci gaba da cewa “Na buga wakokin ne a wani sitidiyo mai suna Musti Studiyo da ke unguwar Zango a Legas. Kuma na fitar da wakokin ne don idan mutane suka ji wani kuskure za su yi mini gyara, saboda wannan shi ne karo na farko da na fitar da albam din wakokin. Tuni na fitar da wakokin domin sayarwa.”
Ya bayyana cewa ya yi wakokin ne saboda dalilai daban-daban da suka sha bamban da juna.
“Ka ga kamar wakar Sarkin samarin Agege na yi ta ne saboda taimakon da yake yi wa mutane, ita kuwa wakar ‘Duniya’ na yi ta ne saboda irin maganganun da mutane suka rika yi a kaina lokacin da na fara harkar fim, sai wakar ‘’Yan Agege’ wace na yi ta saboda girmama manyan Agege, sai wakar ‘Masoya’ da na yi ta saboda budurwata sai wakar ‘KB Yerima’ wacce na yi a kan wani abokina, kuma aminina mai suna Yerima,” inji shi.
Ya kara da cewa burinsa shi ne mutane su ilimantu su koyi darasin da ke cikin wakokin.
Sai dai dankwalisa ya bayyana cewa yanke shawarar shiga harkokin wakoki ne saboda yadda waka take da tasiri a ratuwar dan adam.
“Ta hanyar waka za ka isar da sakonka kai tsaye ya isa zuwa ga jama’a ba tare da wata matsala ba, shi ma fim yana isar da sako amma waka tana da karfi sosai kuma tana da tasiri a zukatan al’umma. Saboda haka ina fata wakokin da na yi za su samu karbuwa ga jama’a kuma su amfanar da su,” inji shi.